Aiyuka 6 da suka fi kawo kudi a Najeriya

Aiyuka 6 da suka fi kawo kudi a Najeriya

Akwai aiyuka da dama a Najeriya da suke kawo wa masu yinsu kudi. Yawancin irin wadannan aiyuka suna bukatar basirar mutum, gogewarsa ko kuma ilimin da yake da shi. Idan mutum yana da daya daga cikin wadannan abubuwa uku, zai iya samun daya daga cikin aiyukan da suke kawo kudi ba tare da bata lokaci ba.

1. Nishadi (jaruman fim da mawaka): Sanannen abu ne cewar harkar masana'antun nishadantar wa na kawo kudi a duk fadin duniya. Masu nishadantar wa na samun miliyoyi daga sana'ar nishadantar da jama'a. Ko a nan gida Najeriya, mawaka irinsu Davido, Wizkid, Rarara, Naziru M. Ahmad da sauransu na samun miliyoyin Naira duk lokacin da suka yi taron rera waka don nishadantar da jama'a ko yabon mai mulki, basarake, attajiri ko dan siyasa.

Haka bangaren jaruman fim da masu shirya fina-finan da suka hada da darektoci da furodusoshi ke samun kudi masu nauyin duk lokacin da suka bayyana ko fitar da sabon fim.

2. Likitanci: Duk da wasu na korafin cewar ba a biyan likitoci da kyau a Najeriya, suna daga cikin jerin ma'aikatan da suka fi daukan albashi me tsoka saboda darajar takardar karatunsu da kuma gogewa. Alal misali, kwararren likita a Najeriya zai iya daukan albashin da ya kai N1m duk wata.

Aiyuka 6 da suka fi kawo kudi a Najeriya
Likita
Asali: Depositphotos

3. Lauya: Ba da zarar mutum ya kammala karatun lauya yake fara samun kudi ba, amma duk da hakan lauyoyin na daga cikin masu samun kudi a Najeriya. Matukar lauya ya kware kuma bashi da tsoro wajen wakilci a kotu, tabbas zai ke samun kudi masu nauyi.

DUBA WANNAN: Kuncin rayuwa: Wani mutum ya banka wa kan sa wuta bayan ya yi korafi da yunwa

4. Tukin jirgin sama: Saboda hatsarin da ke cikinsa, tukin jirgin sama na daga cikin aiyukan dake kawo kudi a fadin duniya. Wata majiya ta ce direbobin jirgi a Najeriya na daukan albashin da ya kai N500,000 zuwa N1m duk wata. Albashin ya sha ban-ban daga kamfani zuwa kamfani.

5. Injiniya: Injiniyoyi, musamman masu aiki da kamfanonin man fetur na samun kudi masu yawa daga aikinsu. Bisa la'akari da bangaren injiniyarin da mutum ya karanta, injiniyoyi na daukan albashin N8m, N10m zuwa N12m duk shekara.

6. Tukin jirgin ruwa: Duk da irin kudin da ke cikin aikin, matukan jirgin ruwa na wuyar samu a Najeriya. Kamar tukin jirgin sama, akwai hatsari a cikin aikin tukin jirgin ruwa.

Tsirarun jami'o'i ne ke koyar da ilimin tukin jirgin ruwa a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng