'Yan bindiga sun sace uwargida da amaryar Alhaji Babaji, jigo a gwamnatin Taraba

'Yan bindiga sun sace uwargida da amaryar Alhaji Babaji, jigo a gwamnatin Taraba

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace matan Alhaji Babaji Dadinkowa, babban sakatare a ofishin mataimakin gwamnan jihar Taraba.

Majiyar mu ta shaida mana cewar 'yan bindigar sun dira a gidan babban sakataren da ke unguwar Yagai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, da tsakar daren ranar Litinin.

'Yan bindigar sun yi harbin iska da ya tsorata jama'ar yankin har suka gudu, kafin daga bisani su shiga gidan babban sakataren.

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan bindigar sun kutsa kai cikin gidan ta karfin tsiya, sai dai a lokacin Alhaji Babaji ba ya cikin gidan.

'Yan bindiga sun sace uwargida da amaryar Alhaji Babaji, jigo a gwamnatin Taraba

Gwamnan jihar Taraba; Darius Ishaku
Source: UGC

Sai dai, duk da hakan, 'yan bindigar sun yi awon gaba da matan sa guda biyu zuwa wurin da ya zuwa yanzu babu wanda ya sani.

DUBA WANNAN: Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, 'yan bindigar basu tuntubu Alhaji Babaji ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da labarin sace matan babban sakataren.

Ya ce rundunar 'yan sanda ta fara aikin ceto matan da kuma cafke 'yan bindigar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel