Shugaba Buhari na ganawar sirri da Sarkin Qatar a garin Abuja

Shugaba Buhari na ganawar sirri da Sarkin Qatar a garin Abuja

Rana dai ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya domin kuwa mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata muhimmiyar ganawa ta sirrance tare da sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim bin Hamad Althani.

Da misalin karfe 12.11 na ranar Talata, 23 ga watan Afrilun 2019, Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim bin Hamad Althani ya iso fadar Villa da ke garin Abuja inda ya samu kyakkyawan karamci na tarba tare da lale maraba ta shugaban kasa Buhari.

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar
Source: Facebook

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar
Source: Facebook

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar
Source: Facebook

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar

Hotuna yayin isowar Sarkin Qatar
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, bayan tarbar girma ta faretin dakarun soji ta tsawon dakika 30, shugaban kasa Buhari tare da babban bako sun shiga cikin ganawa ta sirrance. A na sa ran Sarkin Hamad zai koma birnin Doha da zarar ya karkare musabbabin da ya kawo shi kasar nan.

KARANTA KUMA: Shugabancin Majalisa: Buhari zai gana da zababbun gwamnonin APC

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya gana da Sarkin Qatar yayin da ya kai ziyara birnin Doha a watan Fabrairu na shekarar 2016, inda suka tattauna kan al'amurran da suka shafi ma'adanan man fetur da kasashen biyu ke da arzikin sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel