Kotu ta soke zaben dan majalisar wakilai na APC daga Katsina

Kotu ta soke zaben dan majalisar wakilai na APC daga Katsina

Wata kotun tarayya da ke zaman ta a Katsina ta kwace kujerar mamba a majalisar wakilai daga mazabar Bakori da Danja, Honarabul Aminu Bakori.

Dama kotun ta tsayar da ranar Alhamis a matsayin ranar da zata yanke hukunci a karar da Injiniya Yakubu Nuhu Danja ya shigar gabanta, ya na kalubalantar nasarar da Bakori ya samu a zaben fidda 'yan takara da jam'iyyar APC ta gudanar a watan Nuwamba na shekara 2018.

Danja ya shaidawa kotun cewar Bakori ya zama mamba a majalisar wakilai ta haramtacciyar hanya, tare da rokon kotun ta karba masa nasarar da Bakori ya yi masa fashi.

Bayan ya gabatar da dukkan hujjoji da suka hada da takardar sakamakon zaben fidda 'yan takara, Danja ya roki kotun da ta bayyana shi a matsayin halastaccen dan takarar kujerar majalisar wakilai na mazabar Bakori da Danja.

Kotu ta soke zaben dan majalisar wakilai na APC daga Katsina
Injiniya Yakubu Nuhu Danja
Asali: Twitter

Tun bayan fitar da sunan 'yan takara ne Danja ya yi korafin cewar uwar jam'iyyar APC ta maye sunansa da na Bakori.

DUBA WANNAN: Ba mu kulla yarejejeniyar cire tallafin man fetur da IMF ba - Ministar kudi

A zaben fidda 'yan takarar da aka yi a watan Nuwamba, Danja ya zo na daya da adadin kuri'u 314, yayin da dan majalisa mai ci, Bakori, ya zo na biyu da adadin kuri'u 305, wanda sakamakon hakan ne shugaban kwamitin gudanar da zaben cikin gida da APC ta turo jihar Katsina, Dakta Isah Adamu, ya bayyana sunan Danja a matsayin wanda ya lashe zaben.

Danja ya ce, wasu manya a hedikwatar jam'iyyar APC sun hana kokarin gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da na shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina, Shittu Shittu, na kwato masa hakkinsa ya yi tasiri.

"Hakan ya sa bani da wani zabi da ya wuce na nufi kotu domin ta kwato min hakki na," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel