Wata daliba ta kashe kanta, saboda saurayinta ya rabu da ita

Wata daliba ta kashe kanta, saboda saurayinta ya rabu da ita

- An samu gawar wata daliba a jami'ar jihar Kogi, jim kadan bayan sun samu sabani da saurayinta, inda ya bukaci su rabu

- Rahotanni sun nuna cewa dalibar ta sha guba ne, saboda bakin cikin abinda saurayin ya yi mata

A ranar Larabar nan wata dalibar jami'a dake ajin farko a jami'ar jihar Kogi, Miss Rebecca Michael, ta kashe kanta, jim kadan bayan saurayinta ya rabu da ita.

A rahoton da muka samu, dalibar ta samu damar shiga makarantar a wannan shekarar, inda ta fara karatu a fannin Philosophy a jami'ar.

Marigayiyar, wacce ta kashe kanta a cikin gidan daliban, wanda ke dauke dakuna 200 a garin Lokoja, mun samu rahoton, ta mutu tana da shekaru 20 a duniya.

Wata daliba ta kashe kanta, saboda saurayinta ya rabu da ita
Wata daliba ta kashe kanta, saboda saurayinta ya rabu da ita
Asali: UGC

Bayan ta sha guba, an garzaya da ita asibiti mafi kusa, sai dai kuma ana zuwa ta ce ga garin ku nan.

An binne gawarta jiya Laraba a makabartar Lokongoma, da ke garin Lokoja.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar ya ce har yanzu ba a gabatar da wani rahoto akan lamarin ba.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Jami'in ya yi alkawarin bayyanawa manema labarai, yanda lamarin ya kasance da zarar ya samu rahoto akan lamarin.

Ba wannan ne karo na farko da daliban suke kashe kansu ba ta hanyar shan guba ko rataye kansu.

A kwanakin baya ma wata daliba a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta kashe kanta ta hanyar shan guba, saboda iyayenta suna zargin ita maiyace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel