Mutane sama da 100,000 ne suka cika aikin kwastan daga jiya zuwa yau
- Bayan sanarwar da hukumar kwastan ta bayar na fara daukar aiki a ranar Talatar nan da ta gabata
- Daga jiya zuwa yau an samu sama da mutane 100,000 wadanda suka cikaa aikin, wanda ita kuma hukumar kwastan din ta na bukatar mutane 3,200 kacal
A cikin kasa da awanni 24, bayan hukumar kwastan ta kasa ta bude shafinta na yanar gizo don daukar ma'aikata, an samu sama da mutane 100,000 wadanda suka cika fom din daukar aikin.
Daya daga cikin jami'an hukumar wadanda suke kula da shafin hukumar kwastan na yanar gizo da ke babban birnin tarayya, shine ya bayyana hakan, sai dai jami'in ya bukaci an sakaye sunanshi, inda ya ke cewa a jiya Laraba da misalin karfe 4 na yamma sama da mutane 91,000 suka cika fom din.
Idan ba a manta ba majiyarmu ta kawo muku rahoton cewa hukumar kwastan za ta fara daukar ma'aikata daga ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 12 na dare, inda zata rufe shafin nata nan da sati uku masu gabatowa.
KU KARANTA: Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki
Mataimakin shugaban hukumar kwastan mai rikon kwarya, Umar Sanusi ya bayyana cewa za su dauki mutane 800 wadanda zasu cike gurbi na Superitendent Cadre, sannan mutane 2,400 za a dauke su a matsayin Customs Inspector da Customs Assistant Cadre.
Ya ce shafin hukumar na yanar gizo zai fara aiki daga karfe 12 na daren jiya Talata sannan za a rufe shafin bayan sati uku da bude shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng