Mama Taraba ta temi addu'ar 'yan Najeriya a kan tiyatar da za ai mata

Mama Taraba ta temi addu'ar 'yan Najeriya a kan tiyatar da za ai mata

Tsohuwar ministar Buhari kuma tsohuwar 'yar takarar gwamna a jihar Taraba, Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da 'Mama Taraba", ta nemi addu'ar jama'a a kan tiyatar canjin murfin kokon gwuiwa da za a yi mata.

A wani sako da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta (Twitter), Mama Taraba ta ce an kammala shiri tsaf domin shiga da ita dakin tiyata a asibiti, a saboda haka ta ke neman addu'a.

Mama Taraba ta hada da hotonta a kan gadon asibiti a rubutaccen sakon da ta fitar kamar haka, "an kammala shiri tsaf domin yi min tiyatar canjin murfin kokon gwuiwa, ku saka ni a addu'a. Allah ya kaddara saduwar mu, Amin."

Tsohuwar ministar ta rubuta sakon ne cikin harshen Turanci da Hausa.

Mama Taraba ta ajiye mukaminta na ministar harkokin mata a gwamnatin Buhari tare da fita daga jam'iyyar APC a ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Mama Taraba ta temi addu'ar 'yan Najeriya a kan tiyatar da za ai mata
Mama Taraba a gadon asibiti
Asali: Facebook

Tauraruwar tsohuwar ministar ta fara haska wa a siyasar Najeriya ne bayan tayi takarar neman kujerar gwamnan jihar Taraba a shekarar 2015 a karkashin inuwar jam'iyyar APC, kuma daga wannan takara ne ta samo sunan 'Mama Taraba'.

DUBA WANNAN: Ana shan bakar wuya a mulkin Buhari - Jarumar fim

Dangantaka tsakanin tsohuwar ministar da jam'iyyar APC ta fara tsami ne bayan ta fito ta bayyana goyon bayanta ga takarar Atiku Abubakar bayan ya bar jam'iyyar APC.

Daga bisani ita ma Mama Taraba ta fice daga APC bayan jam'iyyar tayi watsi da kudirinta na son yin takarar gwamna, ta koma jam'iyyar UDP, inda tayi takarar gwamna a zaben da aka yi a watan Maris na shekarar nan da muke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel