Rikici a Kannywood: Amina Amal ta nemi diyyar naira miliyan 50 daga wajen Hadiza Gabon

Rikici a Kannywood: Amina Amal ta nemi diyyar naira miliyan 50 daga wajen Hadiza Gabon

Fitacciyar jarumar Kannywood, Amina Amal ta maka Hadiza Gabon gaban wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Kano akan zarginta da take yi ci mata mutunci, tare da cin zarafinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amal na tuhumar Gabon da ci mata zarafi ne, don haka ta nemi kotun ta bi matahakkinta, tare da bukatar ta tilasta ma Gabon ta nemi afuwarta a fili, wanda take bukaci Gabon ta buga neman afuwar a manyan jaridun kasar nan guda biyu.

KU KARANTA; Gwamnati ta garkame gidajen mai 6 dake boye man fetir a Sakkwato

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito Amal ta nemi kotun ta tilasta ma Hadiza Gabon ta biyata diyyar naira miliyan hamsin (N50,000,000) saboda bata mata suna da tace Hadizn tayi.

Wannan rikici tsakanin Hadiza da Amal ya samo asali ne tun lokacin da Amal ta daura wani hotonta sanye da kaya masu nuna tsiraici a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Instagram, wanda hakan yasa jama’a suka yi tir da ita, tare da Allah wadai.

Daga cikin wadanda suka nuna rashin dacewar daura wannan hoto akwai Hadiza Gabon, wannan tsokaci da Gabon tayi shine ya bata ma Amal rai, inda ta sake daura wani bayani a shafin nata tana zargin Hadiza Gabon da nemanta don suyi madigo.

Sai dai hakan ya janyo cece kuce a tsakaninsu, wanda tasa Gabon ta kamo Amal tare da sanyata a cikin wani bidiyo inda take mata tambayoyi game da wancan zargi da tayi, ita kuma tana bata amsa, a ciki ne Amal ta tabbatar da cewa sharri da kage kawia take yi ma Hadiza.

Duk a cikin kokarinta na wanke kanta, an hangi Hadizan a cikin wani bidiyon tana sharara ma Amal mari akan wannan sharri da tace ta yi mata da nufin bata masa suna, kai har ma da duka, ita kuwa Amal kuka kawai take shekawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng