Yadda na samu kudi daga hannun su Fayose inji Manajan Banki

Yadda na samu kudi daga hannun su Fayose inji Manajan Banki

A jiye ne babban kotun tarayya da ke zama a Legas ta saurari yadda wasu makudan kudi da aka fitar daga ofishin tsohon Mai bada shawara a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki su ka isa zuwa jihar Ekiti.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa tana zargin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da yin sama da wasu makudan kudi har Naira Biliyan 1.2 da kuma wasu Dalar Amurka fam Miliyan 5.

EFCC tana zargin cewa wadannan kudi sun fito ne daga hannun Sambo Dasuki wanda ya rike ofishin ONSA mai ba shugaba Goodluck Jonathan shawara a kan sha’anin tsaro. Yanzu dai kotu ta saurari mai bada shaida na 11 a wannan kara.

Sunday Alade, wanda shi ne Manajan Zenith Bank a lokacin da aka kawo wadannan makudan kudi a 2014 ya bayyanawa Alkali mai shari’a Mojisola Olatoregun yadda ya karbi wadannan kudi. Yanzu dai an dakatar da wannan kara zuwa gaba.

KU KARANTA: Kotu tace IG Wala zai tafi gidan yari na tsawon shekara 12

Yadda na samu kudi daga hannun su Fayose inji Manajan Banki

Tsohon Gwamna Fayose ya musanya zargin laifuffukan da ke kan sa
Source: UGC

“A Ranar 17 ga Watan Yuni ne wani babban Abokin aiki na mai suna Abiodun Oshodi ya kira ni a waya, inda ya nemi in shirya mu je mu karbo wasu kudi da za a sa a cikin asusun bankin mu, don haka mu ka shiya…”

“…Bayan mun yi zaman jira na kusan sa’a guda kenan sai ga wannan Abokin aiki nawa tare da wani Bawan Allah mai suna Abiodun Agbele wanda zai bada wannan kudi, don haka mu ka garzaya zuwa filin jirgi…”

Manajan bankin ya kara da cewa:

“A filin jirgin saman ne mu ka hadu da wasu mutum 3 da su ka fito daga jirgi su ka mika mana wannan makukun kudi, mu ka zuba a cikin mota mu ka dawo cikin banki a Akure tare da jami’an tsaro su na mana gadi…”

Wannan ma’aikacin banki yace da su ka kirga kudin da aka kawo da fari, sun samu Naira Miliyan 724. Daga baya kuma su ka karbi wasu Naira Miliyan 494. Jimillar kudin shi ne Naira Biliyan 1.29 kamar yadda Sunday Alade, ya shaidawa kotu.

Wanan jami’in bankin yace an zuba kudin ne a asusun wasu kamfanoni masu suna De-Privateer, da Spotless Investment da kuma cikin akawun din Ayodele Fayose. Wanda daga baya Hadimin wani Minista ya zo banki ya zari makudan kudin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel