Kishin namiji: Ya bindige budurwarsa har lahira saboda akan zargin cin amana

Kishin namiji: Ya bindige budurwarsa har lahira saboda akan zargin cin amana

Wani matashin saurayi dan shekara 28 mai suna Munabo Tonworio mazaunin unguwar Oluasiri cikin karamar hukumar Nemben jahar Bayelsa ta kira ma kansa ruwa alhalin bashi da lema bayan ya bindige budurwarsa har lahira sakamakon yana zarginsa da cin amanarsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai muni ya faru ne a daren Lahadi, 14 ga watan Afrilu da misalin karfe 11 na dare, wanda hakan ya tayar da hankulan al’ummar wannan unguwa ta jahar Bayelsa.

KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya tayi zarra a tsakanin daliban ABU

Rahotanni sun bayyana cewa Tonworio ya kashe budurwarsa Victoria Ekalamene mai shekaru 35 ne ta hanyar dirka mata harsashi a fuskanta a daidai lokacin da take amsa waya, wayar da yake zargin tana zance da wani saurayinta ne.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Bayelsa, Asinim Butswat ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana yadda lamarin ya auku dalla dalla kamar haka:

“Da misalin karfe 11 na daren Lahadi, 14 ga watan Afrilun shekarar 2019, wani mai suna Munabo Tonworio dan shekara 28 ya bindige buduwarsa mai suna Victoria Ekalamene yar shekara 34 har lahira bayan wata cacar baki data kaure a tsakaninsu a gidan budurwar dake Oluasiri, cikin karamar hukumar Nembe.

“An gano bindigar da yayi amfani da ita wajen kashe budurwar tasa, tuni mun kama saurayin, kuma yana ofishin jami’an SCIID dake garin Yenagoa, inda a yanzu haka ake gudanar da bincike akansa.” Inji shi.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Victoria tana boye saurayin nata a gidanta sakamakon jami’an tsaro suna farautartasa ruwa a jallo saboda hannu cikin ayyukan satar mutane tare da garkuwa dasu a jahar, sai gashi yayi ajalinta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel