Za’a gudanar da zabukan kananan hukumomi mako mai zuwa a Zamfara

Za’a gudanar da zabukan kananan hukumomi mako mai zuwa a Zamfara

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar Zamfara, ZASIEC ta sanar da ranar 27 ga watan Afrilun 2019 a matsayin ranar da zata gudanar da zabukan kananan hukumomi a jahar gaba daya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar, Alhaji Garba Muhammad ne ya bayyana haka a babban birnin jahar Zamfara, Gusau a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a siyasar jahar.

KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya da tayi zarra a tsakanin daliban ABU

Za’a gudanar da zabukan kananan hukumomi mako mai zuwa a Zamfara
Zabe a Najeriya
Asali: UGC

Tun a ranar 2 ga watan Janairun 2019 ne wa’adin mulkin shuwagabannin kananan hukumomi dana Kansilolin jahar ya kare, amma majalisar dokokin jahar ta tsawaita musu wa’adin zuwa ranar 2 ga watan Mayun 2019.

“Mun shirya wannan taro ne don sanin muhimmancinsa, da kuma shirin samar da zaben gaskiya da gaskiya a zaben kananan hukumomin dake karatowa, akwai bukatar daidaikunmu da kuma kungiyoyinmu mu taka rawar data kamata.

“Don haka nake kira ga jam’iyyun siyasa, yan takarkaru dasu fara gudanar da yakin neman zabe, gangamin siyasa da kuma gudanar da zaben fidda gwani, hakanan ina kira ga jami’an tsaro dasu tabbata sun samar da isashshen tsaro a gabani da bayan zaben.” Inji shi.

Shugaban hukumar ya bada tabbacin sun samu dukkanin gudunmuwar kudi da suke gabata na gudanar da zaben daga gwamnatin jahar, don haka zasu fara wayar da kawunan jama’a game da muhimmancin zaben ta hanyar amfani da kafafen watsa labaru da taruka.

Daga karshe ya bayyana ma mahalarta taron cewa a yanzu haka sun kammala aikin horas da jami’a zabe, tare da turasu rumfunan zaben da zasu gudanar da aikinsu a kananan hukumomin jahar, sai dai jam’iyyar PDP ta kaurace ma taron kwata kwata.

Jahar Zamfara dai na fama da matsanancin matsalar tsaro da yaki ci yaki cinyewa, inda a yanzu haka ake kididdigan sama da mutane dubu uku, 3000, da rayukansu suka salwanta sakamakon hare haren yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng