Kasar Amurka ta gargadi 'yan kasarta a kan zuwa Najeriya

Kasar Amurka ta gargadi 'yan kasarta a kan zuwa Najeriya

Kasar Amurka ta gargadi 'yan kasar ta suyi takatsantsan da zuwa Najeriya saboda yawaitar miyagun laifuka kamar fashi da makami, satar motar, ta'addanci, garkuwa da mutane, fyade, zalunci da sauransu da su ka zama ruwan dare a kasar.

A cikin wata sanarwa da Amurka ta fitar a intanet ta sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu alamar 'K' ga matafiyya, ma'anna mutane ke fuskantar barazanar a sace su ko ayi garkuwa da su.

"Sabon alamar na 'K' yana daya daga cikin bayanai da muka bawa 'yan kasar mu masu tafiye-tafiye saboda su dauki matakin da ya dace kafin su tafi kasashen duniya," inji Amurka.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Kasar Amurka ta gargadi 'yan kasarta a kan zuwa Najeriya

Kasar Amurka ta gargadi 'yan kasarta a kan zuwa Najeriya
Source: UGC

"Sauran kasashen da aka sakawa alamar gargadi na 'K' da ke nuna yawaitar satar mutane ko garkuwa da su sun hada da: Afghanistan, Algeria, Angola, Bangladesh, Burkina Faso, Kamaru, Central African Republic, Colombia, Democratic Republic of the Congo, Ethiopia, Haiti, Iran, Iraq, Kenya, Lebanon, Libya, Malaysia, Mali, Mexico, Niger, Najeriya, Pakistan, Papua New Guinea, Philippines, Rasha, Somalia, South Sudan, Sudan, Syria, Trinidad and Tobago, Turkey, Uganda, Ukraine (bangaren da ke karkashin Rasha), Venezuela, da Yemen.

A cikin Najeriya, kasar ta Amurka ta ce jihohin Borno, Yobe da Adamawa ne suka fi hatsari.

"Kungiyar 'yan ta'adda a Arewa maso Gabas su kan kai hare-hare a coci, makarantu, masallatai, ofishohin gwamnati, makarantu da wuraren shakatawa. A kalla 'yan Najeriya Milliyan Biyu ne suka rasa muhallinsu sakamakon ta'addancin da ake yi a Arewa maso Gabashin Najeriya."

Kasashe 35 ne Amurka ta lissafa a matsayin wadanda ke tattare da hatsari ga matafiya.

Hakan ya sa ta shawarci 'yan kasar ta suyi takatsantsan ko su dage tafiyar ko kuma su fasa tafiyar baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel