Yanzu-yanzu: Tankar mai ta kone mutane 10 a jihar Gombe

Yanzu-yanzu: Tankar mai ta kone mutane 10 a jihar Gombe

Yanzun nan wata tankar mai ta fashe a jihar Gombe, inda ta yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane goma, sannan ta kone motoci masu yawan gaske

Sama da mutane goma ne suka rasa ransu, sanadiyyar fashewar tankar mai a garin Gombe yau Asabar dinnan da rana.

Bayan asarar rayukan tankar ta yi sanadiyyar kone motoci masu yawan gaske akan hanyar.

Yanzu-yanzu: Tankar mai ta kone mutane 10 a jihar Gombe

Yanzu-yanzu: Tankar mai ta kone mutane 10 a jihar Gombe
Source: Facebook

Wani wanda abin ya faru akan idon shi ya bayyana cewa, wata tankar mai dauke da man fetur sunyi taho mu hade da wata babbar wacce ta ke dauke da ruwa a cikinta, akan babbar hanyar fita daga garin Gombe.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa sama da mutane goma ne suka rasa rayukan su, inda kungiyar taimakon gaggawa ta dauke gawarwakinsu daga wurin.

A yanzu haka dai jami'an kashe gobara na jihar Gombe suna aiki ba kama hannun yaro don ganin sun shawo kan wutar da ta ke ci ba kakkautawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel