Babbar mota ta hallaka wata daliba jim kadan bayan ta biya kudin makaranta a banki

Babbar mota ta hallaka wata daliba jim kadan bayan ta biya kudin makaranta a banki

- Hatsarin Keke napep da wata babbar mota yayi sanadiyar ran wata daliba har lahira a garin Oyo

- Dalibar mai karatu a Jami'ar Ibadan ta gamu da ajalintane jim kadan bayan ta bar banki inda taje biyan kudin makaranta ranar Juma'a

A ranar Juma’a ne dalibar mai suna Balkis Adeniyi dake Tsangayar kimiyya ta Jami’ar Ibadan ta hadu da ajalinta cikin wani hatsarin daya auku akan titin Mokola-Oyo a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Wani wanda lamarin ya faru akan idonsa ya shaidawa yan jarida hatsarin yayi sanadiyar mummunan rauni ga wasu mutum biyu yayinda mashin mai taya uku wanda akafi sani da ‘Keke Napep’ ya watsa aguje cikin babbar motar zubar da shara a unguwar Leventis dake Sango cikin babban birnin jihar.

Hatsarin adaidaita
Hatsarin adaidaita
Asali: UGC

KU KARANTA:Hanashi takarar gwamna: Kotu ta yi watsi da karar da Ministan sadarwa, Shittu ya shigar kan APC

Bugu da kari, hatsarin dai ya auku ne misalin karfe tara da rabi yayinda dalibar ke barin banki bayan da ta riga ta biya kudin makarantarta.

Hakazalika, jami’an yan sanda sun bayyana lambar keken kamar haka RU 152 UP kana kuma sun fadi sanfarin ita babbar motar wato ‘MARC LAMMERTYN’.

Har wa yau, zance daga bakin wani wanda wannan hatsarin ya faru akan idonsa yace, “Ita dai wannan matar ta fito ne daga banki dake Ajibade inda taje biyan kudin makaranta yayin da wannan abu ya faru.

“Hakika an samu ganin wayarta da kuma jakarta. A dai dai wannan lokacin ne muka samu damar bincika jakarta inda muka samu katinta na Jami’ar Ibadan daga bisani kuma muka nemi iyayenta domin sanar dasu halin da yarsu ke ciki.

“Su kuwa sauran mutum biyu da suka samu raunuka a kai da kafa anyi gaggawar kai su asibiti domin basu taimakon gaggawa.”

Yayinda yake tabbatar da aukuwar wannan lamari, jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar Oyo, mai suna Olugbenga Fadeyi, ya gaskata wannan lamari inda yake cewa tabbas wannan ya hatsarin ya auku.

“Ya sake cewa, DPO na ofshin yan sandan dake Mokola ne ya labarta mana wannan batu inda nan take muka fara gudanar da bincike kai tsaye akan yanda abin ya faru.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel