Zaben Bindow: Lamido bai gayyaci matsafa ba - Masarautar Adamawa

Zaben Bindow: Lamido bai gayyaci matsafa ba - Masarautar Adamawa

Ofishin hulda da jama'a na masarautar Adamawa ta karyata cewa Sarkin Adamawa mai ci a yanzu, Muhammadu Musdafa ya gayyaci wasu makafi uku daga kasar Burkina Faso domin suyi tsibbu na samun nasarar Gwamna Mohammed Jibrilla Bindow a zaben ranar 9 ga watan Maris.

Masarautar ta ce babu gaskiya cikin labarin da Ibrahim Mustapha wanda akafi sani da Baba 10 ya wallafa a wata jarida inda ta ce yunkuri ne kawai ba ta sunnan masarautar saboda fushin shan kaye a zabe.

Zuriyar ta Malam Modibbo Adama sun ce labarin an kirkiro labarin 'makafi uku ne' domin a shafawa Lamidon Adamawa da masarautar kashin kaza.

Zaben Bindow: Lamido bai gayyaci matsafa ba - Masarautar Adamawa
Zaben Bindow: Lamido bai gayyaci matsafa ba - Masarautar Adamawa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Ta kuma karyata cewa an tilastawa al'ummar Adamawa amincewa da Lamidon Adamawa na yanzu inda ta ce kwamitin masu nadin sarauta ne suka zabe shi kuma gwamnatin jihar ta amince da nadinsa a watan Maris na 2010.

"Bisa ga dukkan alamu, nasarar da jam'iyyar PDP ta samu a zaben gwamna da aka kammala a jihar Adamawa cikin 'yan kwana kin nan ne ya bawa marubucin damar kitsa sharri da makirci a kafar yadda labarai.

"Marubucin wanda dan wata jam'iyyar siyasa ne ya fusata saboda nasarar da dan takarar jam'iyyar PDP ya samu a jihar," inji sanarwar.

Masarautar ta bukaci marubucin ya nemi afuwar ta a rubuce idan kuma ba haka ba ya fuskanci shari'a.

Cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, wacce Aminu Usman Nyibango ya rattaba wa hannu a madadin masarautar, ta ce, ta bada mako guda ga Baba 10 da ya bayar da hakuri kuma ya janye zargin da ya yi wa masarautar a jaridu ko kuma ya fuskanci kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel