Mun aminta da matakin karatu na shugaba Buhari - INEC

Mun aminta da matakin karatu na shugaba Buhari - INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta ce ta gamsu da matakin karatu na shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gabatar cikin takardu na shaidu yayin neman takara ta kejerar jagorancin kasar nan.

Babbbar hukuar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta ce ta gamsu da takardu na shaidar matakin karatu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar yayin neman takarar kujerar shugabancin kasar nan.

Mun aminta da matakin karatu na shugaba Buhari - INEC

Mun aminta da matakin karatu na shugaba Buhari - INEC
Source: Facebook

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, matakin karatu na shugaban kasa Buhari ya zamto lamari na takaddama cikin korafi na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar a gaban Kuliya.

Tawagar Lauyoyi mai neman hakki a madadin Atiku, ta shigar da korafin cewa ba bu wata makaranta makamanciyar wadda shugaban kasa Buhari ya yi ikirarin halarta wajen samun matakin ilimi na Sakandire.

KARANTA KUMA: Gobara ta kone shaguna 6 a babbar kasuwar jihar Kebbi

Yayin martanin wannan tuhuma, hukumar INEC ta ce ko kadan ba ta da wani haufi kuma ta gamsu da matakin karatu na shugaban kasa Buhari da ke tabbatar da cancantar sa ta neman rike akalar jagorancin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel