Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda (Hotuna)

Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda (Hotuna)

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun samu nasarar kama wani gagararren dan fashi da kuma mai garkuwa da mutane da suka dade suna farautarsa mai suna Shehu Usman, a jahar Ondo, inji rahoton Sahara reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu ne Yansanda suka bayyana Shehu ga manema labaru a babban ofishin Yansanda dake garin Akure na jahar Ondo, tare da abokan aikinsa guda hudu.

KU KARANTA: Kifa daya kwala: Yadda dan dambe ya sumar da budurwa tsawon kwanaki 2 da naushi daya

Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda (Hotuna)
Shehu
Asali: UGC

Da yake bayyanasu ga manema labaru, kwamishinan Yansandan jahar, Undie Adie ya bayyana wadanda aka kama tare da Shehu sun hada da Ismaila Wakili mai shekaru 19, Abdullahi Sani 33, Mohammed Abdullahi 36 da kuma Umaru Usman mai shekaru 25.

Kwamishinan ya kara da cewa gungun yan fashin sun dade suna fitinar jama’an yankin Auga na jahar Ondo, Kabba na jahar Kogi da Ibilo na jahar Edo, da fashi da kuma satar mutane don neman kudin fansa dasu.

Sai dai wata majiya daga rundunar Yansandan ta bayyana cewa har yanzu basu samu nasarar kama jagoran wadannan yan fashin ba, wanda yace a yanzu haka ya tsere, amma ya bada tabbacin zasu kamashi nan bada jimawa ba.

Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda (Hotuna)
Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda
Asali: UGC

Da yake bayanin yadda suka kama yan fashin, kwamishinan Yansanda Adie yace “Dubunsu ta cika ne bayan sun kama Prince Omoghae Igbegbon, inda suka kwace masa N180,000, sa’annan suka nemi a biyasu kudin fansa N30,000,000.

“Daga nan sai Yansanda da wasu yan banga suka bi sawunsu zuwa cikin dajin da suke rike dashi, inda aka yi bata kashi da musayar wuta, wanda yasa suka saki Prince suka tsere, shi kuma ya nemi mafaka a wani kauyen Ibilo.

“Daga nan muka nemi jama’an kauyukan dake yankin dasu kawo mana rahoton duk wani bakon fuska da suka gani, wanda basu saba gani ba, a haka Princie ya gane Wakili, inda muka kamashi, kuma ya amsa laifinsa, sa’annan ya kaimu zuwa inda sauran suka boye a Aduwawa cikin garin Bini.” Inji shi.

Daga karshe yace sun kwato bindigu guda hudu samfurin Double barrel, single barrel, da pump action da layu da dama, sa’annan yace zasu gurfanar dasu gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike akansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel