Buhari ya bayyana wasu mutane biyu masu rikon amana a lokacin da yayi mulkin soja

Buhari ya bayyana wasu mutane biyu masu rikon amana a lokacin da yayi mulkin soja

- A lokacin da ya yi mulkin soja shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha fama da, barayin gwamnati, inda ya dinga kama su yana jefawa gidan kurkuku

- Sai dai kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wasu mutane biyu masu gaskiya da rikon amana da ya yi aiki da su a lokacin mulkin shi na soja

A jiya Talata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, mutum biyu ne kawai ya samu masu amana a lokacin da aka kama jami'an gwamnatinsa da laifin cin hanci a lokacin da ya yi mulkin Soja a Najeriya.

Da ya ke jawabi a lokacin da ya ke ganawa da 'yan Najeriya mazauna Dubai, shugaban ya tuna yadda ya tura tsohon shugaban kasa Marigayi Shehu Shagari da sauran manyan jami'an gwamnati zuwa gidan yari, saboda kama su da aka yi da laifin cin hanci da rashawa, ya ce mutum biyun nan ne kawai ban same su da laifi ba a lokacin, Bilyaminu Usman, wanda ya yi karamin minista a lokacin dan jihar Jigawa, sai kuma Adamu Chiroma, wanda ya yi ministan kudi a lokacin kuma ya yi gwamnan babban bankin Najeriya, su ne kadai aka samu ba su da laifin cin hanci da aka bincike su.

Buhari ya bayyana wasu mutane biyu masu rikon amana a lokacin da yayi mulkin soja

Buhari ya bayyana wasu mutane biyu masu rikon amana a lokacin da yayi mulkin soja
Source: Depositphotos

A lokacin da shugaban kasar ya ke amsa tambayar wani dan Najeriya a Dubai din, mutumin ya tambayi shugaban kasar: "Wane irin kokari kake yi domin kawo karshen cin hanci da kuma hukunta wadanda aka kama da laifin cin hanci a yanzu? Saboda mutane da yawa suna cewa, sai dai kawai ka fita ka yi ta surutu amma ka kasa daukan mataki akan barayin dukiyar gwamnatin."

KU KARANTA: Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

Shugaban kasar ya bai wa mutumin amsa kamar haka: "Na taba yin mulki a kasar nan, wasu daga cikinku sun san lokacin da na yi mulkin soja, lokacin bani da aiki da ya wuce kama barayin gwamnati, tun daga kan shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, ministoci da sauran su, duk sai dana tura su gidan kurkuku, sannan na fada musu cewar ana zargin su da laifin cin hanci da rashawa. Sannan na bayyana musu bazan sake su ba har sai sun fito sun tabbatar da cewa ba su da laifi.

"A lokacin mutane biyu ne kawai muka samu wadanda suke da amana, amma dukansu sun rigamu gidan gaskiya, akwai karamin minista, Bilyaminu Usman, daga jihar Jigawa, sai kuma Adamu Chiroma, ministan kudi sannan kuma gwamnan babban banki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel