Sarkin Musulmi ya nemi hukumar 'yan sanda ta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Sarkin Musulmi ya nemi hukumar 'yan sanda ta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Sarkin Musulmi Mai Martaba Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad, ya yi kira na gargadin hukumar 'yan sandan Najeriya da ta gaggauta zage dantsen ta wajen kawo karshen kashe-kashe da miyagun ababe na ta'addanci a fadin kasar nan.

Sarkin Musulmi ya nemi hukumar 'yan sanda ta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Sarkin Musulmi ya nemi hukumar 'yan sanda ta kawo karshen ta'addanci a Najeriya
Source: UGC

Yayin bayar da shaidar wannan furuci cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya ce Sarkin Musulmi ya sha alwashin bayar gudunmuwa daidai iko tare da goyon bayan hukumar 'yan sanda wajen sauke nauyin da rataya a wuyan ta.

Sultan na Sakkwato ya yi alwashi a fadar sa ta Gidan Sarkin Musulin da ke birnin Shehu yayin da mukaddashin sufeton 'yan sanda, Muhammad Adamu ya ziyarci fadar sa cikin tawagar Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, Mataimakin sa Alhaji Mannir Dan'iya da kuma sauran kusoshin gwamnati gami da manyan jami'an tsaro na 'yan sanda.

KARANTA KUMA: An bayyana masu zartar da ta'addanci a jihar Zamfara

Sarkin Musulmi ya sha alwashi tabbatar da hadin gwiwar kungiyar Sarakunan gargajiya ta Najeriya domin goyon bayan hukumomin tsaro wajen yakar miyagun ababe masu barazana da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Kazalika Sarki musulmi ya yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da su tashi tsaye wajen bayar da duk wata gudunmuwa ga hukumomin tsaro yayin yunkurin su na tsarkake kasar nan daga munanan ababe na ta'ada masu ci karo da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel