Shekara biyun bayan mutuwar matar sa, Danjuma Goje ya angonce

Shekara biyun bayan mutuwar matar sa, Danjuma Goje ya angonce

- Rahotanni sun bayyana cewar Sanata Danjuma Goje ya angonce da wata matashiya

- Tsohon gwamnan kuma tsohon karamin ministan tama da makarfa, ya angonce ne bayan shekara biyu da mutuwar matar sa

- Tsohuwar matar Goje ta mutu ne a wani asibitin kasar Amurka a watan Oktoba na shekarar 2017

Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattijai, Danjuma Goje, ya auri wata matashiya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hajiya Yelwa, tsohuwar matar Sanata Goje ta mutu ne a watan Oktoba na shekarar 2017 bayan tayi fama da gajeriyar jinya. Ta mutu tana da shekaru 55 a duniya.

Shekara biyun bayan mutuwar matar sa, Danjuma Goje ya angonce

Danjuma Goje ya angonce
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewar sabuwar amaryar 'yar asalin jihar Bauchi ce. Labarin auren Goje da matashiyar ya fara yaduwa ne a dandalin sada zumunta. A cikin wani faifan bidiyo, an ga sabuwar amaryar tare da wasu 'yan uwanta suna fito wa daga cikin wani jirgi.

DUBA WANNAN: Hanyar lafiya: Abubuwa 10 da ya kamata ku kiyaye lokacin zafi

Auren na Sanata Goje da matashiyar amaryar sa, na zuwa ne bayan cikar shekaru biyu da mutuwar matar sa.

Sanata Goje na daga cikin mambobin jam'iyyar APC da ke sansana kujerar shugaban majalisar dattijai. Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewar wannan kudiri bayan shugaban kasa da mataimakinsa da shugaban jam'iyya sun lallabe shi domin ya janye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel