Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin Duniya ta bayyana wanda zai gaji Buhari a 2023

Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin Duniya ta bayyana wanda zai gaji Buhari a 2023

Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, kuma tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya, Hajiya Amina Mohammed ta bayyana cewa mace ce zata gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan karewar wa’adin mulkinsa a shekarar 2023.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Amina ta bayyana haka ne yayin da take tattaunawa da hamshakin attajirin nan dan Afirka, Mo Ibrahim, inda tace zata zamto shugabar yakin neman zaben wannan matar idan lokaci yayi.

KU KARANTA: Farfesa Mohammed: Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta samu sabon shugaba

Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin Duniya ta bayyana wanda zai gaji Buhari a 2023

Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin Duniya, Amina.
Source: Depositphotos

Da fari dai Mo Ibrahim ne ya fara tambayarta ko akwai yiwuwar mace ta zama shugabar kasar Najeriya, kuma yaushe ne? sai ta kada baki tace “2023 da ikon Allah.”

Da ya kara tambayarta ko za ta nemi takarar shugaban kasa sai tace “Hidima nake yi ma jama’a a duk rayuwata, don haka bani da matsala da yin hakan.

“Amma maganar gaskiya shine, ina kallon kaina a matsayin wanda za’a iya nadawa mukami, ba wai wanda zata iya tsayawa takara ko a zabeta ba, na gamsu da Dimukradiyya, amma da kamar wuya mace ta ratso wannan fagen ta zama shugabar kasa.” Inji ta.

Da take tsokaci akan nasarar da Buhari ya samu a zabe kuwa, Amina ta dangantashi da wani lamari mai ban mamaki da daure kai saboda ba karamin gwagwarmaya ya sha ba kafin a kai ga wannan nasara.

“Samun shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa kadai wani lamari ne da za’a iya dangantashi da mu’ujiza, saboda ba kasafai aka fiya samun irin haka a Najeriya ba. Har yanzu Dimukradiyyarmu tana dabo ne, don haka nake ganin zan iya zama shugabar yakin neman zabe ga macen da zata gaji Buhari.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel