Adam Zango ya shiga rigima da masu zagin mahaifiyar sa

Adam Zango ya shiga rigima da masu zagin mahaifiyar sa

Fitaccen jarumin masana'antar shirya wasan fina-finan Hausa (Kannywood), Adam Zango, ya ja layi tsakaninsa da masu zagi ko cin mutuncin mahaifiiyar sa da ke ciki ko wajen masana'antar Kannywood, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Jarumi Zango ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta (Instagram), "uwa ba ta fi uwa ba, tunda ka saka yaranka sun zagi mahaifiyata, tabbas ni ma zan zagi ta ka. Na zuba ido domin ganin ko zaka tsawatar wa yaranka amma baka yi hakan ba."

A rubutun na Zango, ya ambaci (tagging) shafin jarumi Ali Nuhu, lamarin da ya haddasa zargin cewar yana nufin Ali Nuhu da kalamansa.

A wani sakon daban, Zango ya rubuta, "na dauki hoton duk wani zagi da kayi min kuma zan rama daya bayan daya, sai mu ga waye ya fi iya rashin mutunci a Kannywood."

Kafin faruwar hakan, Zango ya saka wani faifan bidyo dake nuna wasu furodusohi biyu; Aminu Bala da Kawu Kamfa, suna zagin wani da basu ambaci sunansa ba.

Adam Zango ya shiga rigima da masu zagin mahaifiyar sa

Adam Zango da Ali Nuhu
Source: Facebook

A faifan bidiyon, an ji Aminu na yi wa wani gargadin cewar, shi ya na girmama mahaifiyar sa.

Sai Kamfa ya katse shi ta hanyar cewar wanda ake magana a kansa ba ya ganin girman mahaifiyarsa, saboda ko kiranta ba ya dauka.

DUBA WANNAN: Allah kyauta: An kashe mutane 20 a sabon harin 'yan bindiga a Kajuru

NAN ta rawaito cewar ko a shekarar da ta gabata sai da aka samu kwatankwacin irin wannan rikici tsakanin Ali Nuhu da Zango.

Rikicin ya lafa ne bayan Ali Nuhu ya yi kira ga magoya bayansa da ke ciki da wajen Kannywood da su guji haifar da rashin jituwa tsakaninsa da duk wani jarumin Kannywood. (NAN).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel