Allah kyauta: An kashe mutane 20 a sabon harin 'yan bindiga a Kajuru

Allah kyauta: An kashe mutane 20 a sabon harin 'yan bindiga a Kajuru

A kalla mutane 20 ne rahotanni suka bayyana an kashe a sabon harin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai kauyen Angwan Aku dake karkashin karamar hukumar Kajuru a jhar Kaduna.

Wani cikin mazauna garin ya shaida wa majiyar mu cewar, 'yan bindigar bindiga cikin kayan soji da bindigu samfurin AK47 da wukake da sanduna sun kai harin da misalin karfe 7:00 na daren Litinin.

Majiyar ta ce mutanen sun bude wuta a kan jama'ar garin ba tare da banbance babba ko karami, mace ko namiji ba.

Bayan mutanen da suka mutu, da dama sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

Allah kyauta: An kashe mutane 20 a sabon harin 'yan bindiga a Kajuru

Gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-Rufa'i
Source: UGC

A cewar majiyar, "masu harin sun shigo garin bagatatan tare da fara harbin jama'a ba tare da tantance wa ba. Duk mun bazama, mun shiga jeji. Amma ko a lokacin da muke gudu domin tsira da rayuwar mu, sun cigaba da binmu tare da harbinmu, har cikin jejin suka biyo mu suka kashe wasu.

"Wasu daga cikinsu na sanye da kayan sojoji da rigar garkuwa daga harbin bindiga, na hange su daga inda nake a boye."

DUBA WANNAN: Rundunar sojin sama tayi kasa-kasa da mafakar ISWAP a Tumbun Zarami, da yawa sun mutu

Majiyar tayi zargin cewar, jami'an 'yan sanda sun zo kauyen cikin motoci kirar Hilux guda 8, amma sun kasa shiga daji domin bin sahun 'yan bindigar

"Tawagar 'yan sanda a cikin Hilux 8 sun zo a lokacin da 'yan bindigar ke kan kaddamar da harin, amma a maimakon su bi 'yan bindigar cikin dajin da suka ruga, sai kawai suka juya," a cewar majiyar.

Majiyar tayi zargin cewar tun sain da ya gabata ake rade-radin za a kai harin, kuma gwamnatin jihar Kaduna ta samu labari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel