Dubai: Buhari ya shiga zawarcin masu saka hannun jari a Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da kungiyoyi 6 na masu saka hannun jari bayan kammala taron masu saka hannun jari na wannan shekara da aka yi a Dubai.
A jawabin da Femi Adesina, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya aika sako daya ga masu saka hannun jarin: "Ku zo Najeriya domin samun riba a kasuwancinku cikin kankanin lokaci."
Sheikh Ahmed Al Maktoum, dan cikin gidan sarautar kasar Dubai kuma daya daga cikin masu saka hannu jari, ya nuna sha'awarsa ta kafa cibiyar samar da hasken wutar lantarki a Legas.
Mista Yusuff Ali, shugaban kamfanin 'Lulu Group' masu manyan shagunan kayan sayar wa a yankin gabsa ta tsakiya da Asia, ya nuna sha'awarsa ta hada gwuiwa da manoma a Najeriya domin samun kayan amfanin gona masu inganci da tsafta. Rukunin shagunan 'Lulu' na da ma'aikata fiye da 50,000.
A wurin taron, akwai Sheikh Hussain Al Nowais, shugaban cibiyar samar da wuta ta 'Amea Power' da rukunin Otal din 'Rotana', wanda kuma ya nuna sha'awarsa ta gina Otal a Najeriya.
DUBA WANNAN: Kara kudin tikiti: EFCC ta kama ma'aikatan tashar jirgin kasa 5 a Kaduna, sunaye
Sheikh Rashid Ali Rashid Lootah, shugaban kamfanin dillancin gidaje da filaye a kasar Dubai, ya shaida wa shugaba Buhari cewar kamfaninsa na da sha'awar fadada kasuwancinsa zuwa Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng