Na san manyan arewa da ke da hannu a kisan rayuka a Zamfara - Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta, Datti Assalafi, ya wallafa wani jawabi da limamin masallacin unguwar Gadon Kaya, Sheikh Abdallah, ya yi a cikin wani faifan bidiyo da aka nada yayin da yake magana a kan kisan rayukan da ake yi a jihar Zamfara.
"Bari na fada muku wani sirri, zamu fada don ya yadu saboda manya suji, wani zai yi tambaya wai me yasa aka mayar da hankali akan Zamfara ake ta kashe mutane?
"Wato akwai wasu ne daga cikin manyan Kasarnan, lokacin fadar sunansu bai yi ba, amma na sansu, manya ne kuma 'yan arewa ne, suna da ra'ayi akwai arziki ne a jihar Zamfara, ana diban zinare da arzikin dake karkashin kasa da ake tonowa, don haka manyan su suke da hannu wajen diban kayan arzikin suna fitar dasu kasashen waje suna samun dunbin dukiya
"Idan aka bar mutane hankalinsu ya kwanta za'a dinga ganin ana fita da dukiya, don haka za'ayi magana, to yanzu sai aka mayar da gurin a tayar da hankalinsu, yanzu mutanen gurin ta rayukansu suke da dabbobinsu da abincin da zasuci su rayu, can kuma inda ake diban arzikin suna can suna diba wallahi, wannan shine abinda yake faruwa a Zamfara.
"Kuma abin yana da alaka da manya ne shiyasa abin yaki cinyewa, suna da alaka da sojoji, suna da alaka da Gwamnoni suna da alaka da jami'an tsaro, duk wani babba da yake wannan jihar ta Zamfara idan ma zaiyi magana akan kisan da akeyi to akwai wani abu da ake tsakura masa a bashi toshiyar baki, don haka gwanda suyi ta kashe mutane a kasa samun zaman lafita suyi ta diban arziki.
DUBA WANNAN: Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin kasa
"Yanzu kamar rikicin da akayi a Borno, Sambisa da sauransu akwai fetur ne a gurin, akwai arziki ne a gurin, idan aka bari hankali ya kwanta ba'ayi ta fadace fadace ba to ai hankali zai koma ace gwamnati taje ta fara diban wannan arzikin don mutane su amfana.
"Duk abinda kuka ga anayi na zubar da jinin mutane a Kasarnan wallahi akwai hannun musulmai 'yan arewa manyan Kasarnan akwai hannunsu a ciki, kawai munafurci ne ake ba'a fada
Yanzu da zaran mutun ya tara mutane ya fadi gaskiya sai a turo jami'an tsaro su tafi da mutum don basa so a fadi gaskiya, amma a matsayin mu na 'yan Kasa wajibi mu fadi gaskiya ko zasu kashe mu", Inji Dr. Abdullah Gadan Kaya.
Saurare shi a cikin wannan faifan bidiyo:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng