Kabiru da Farouq; Uba da 'da sun yiwa yarinya mai shekara 13 ciki

Kabiru da Farouq; Uba da 'da sun yiwa yarinya mai shekara 13 ciki

Kabiru; wani mutum mai shekaru 44, da dan cikinsa Farouq; mai shekaru 19, sun shiga hannun dakarun 'yan sanda a jihar Legas bayan samun su da laifin yin fyade tare da yin ciki ga wata matashiya mai shekaru 13 da ba a bayyana sunanta ba.

Lamarin ya faru ne yayin da yarinyar ta ziyarci 'yar uwarta dake auren Kabiru har ta shafe tsawon watanni hudu a gidansu mai lamba 1 dake rukunin gidajen Egbeda a kan titin Olatikupo.

An gano cewar yarinyar ta sha rahoton abinda Kabiru ke yi ma ta ga 'yar uwarta amma ba ta taba daukar wani mataki ba, kafin daga bisani Farouq ya fara kwanciya da ita bayan wata rana ya kama su turmi da tabarya tare da mahaifinsa

Bayan yarinyar ta gaji da cin zarafinta haddi da Kabiru da Farouq ke yi, sai yarinyar ta gudu wurin mahaifiyar ta a jihar Ogun. Bayan an saka ta a makaranta ne wani malami ya gano cewar tana dauke da juna biyu.

Kabiru da Farouq; Uba da 'da sun yiwa yarinya mai shekara 13 ciki
Wasu 'yan sanda a jihar Legas
Asali: UGC

Bayan gano hakan ne, sannan yarinyar ta kwashe labarin abinda ya faru da ita a gidan 'yar uwarta a Lega ta fada wa mahaifiyar ta, lamarin da ya sa mahaifiyar ta shigar da korafi a ofishin 'yan sanda.

A cewar yarinyar, Kabiru ya fara yi mata fyade ne a wani lokaci a cikin a watan Oktoba bayan ya aiketa ta debo masa ruwa.

"Ya aike ni na debo masa ruwa na kai masa bandaki don ya yi wanka. Bayan na kawo ruwan sai ya tura ni cikin bandakin ya yi min fyade. Tun daga wannan lokacin, kusan kullum sai ya yi min fyade. Na fada wa anti na amma ba ta dauki wani mataki a kai ba.

DUBA WANNAN: Satar mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna: Matafiya sun koma tafiya a jirgin sama

“Haka ya cigaba da yi min fyade tunda matar sa ba ta dauki wani mataki ba. Sannan, a watan Janairu, sai Farouq shi ma ya fara bayan ya kama mahaifinsa yana yi min fyade," yarinyar ta fada wa kungiyar kare hakkin yara ta CPN (Child Protection Network).

Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Bala Elkana, ya ce an shigar da korafin yiwa yarinyar fyade a ranar 27 ga watan Maris.

"Mun gurfanar da mutanen biyu a gaban kotun majisatare ta biyu dake Ogba. Yanzu haka suna zaman kaso gidan yarin Kirikiri kafin ranar 13 a watan Mayu da za a cigaba da sauraron karar su," a cewar Elkana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel