An danne mana hakki a zaben gwamnan jihar Sakkwato - APC
Biyo bayan nasarar Gwamna Aminu Tambuwal na jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Sakkwato, shugaban kungiyar yakin neman zaben kujerar gwamna na jam'iyyar APC a jihar, Yusuf Suleiman, ya yi ikirarin an danne masu hakki.
Jagoran kungiyar yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar Sakkwato na jam'iyyar APC, Alhaji Yusuf Suleiman, ya ce ba za su lamunci a rashin adalci ba da cewar za su yi iyaka bakin kokari wajen neman hakki a shari'ance.
Alhaji Suleiman ya bayyana hakan cikin wata hirar sa da manema labarai, inda ya yi ikirarin cewa jam'iyyar adawa ta PDP tare da hadin gwiwar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC sun ci karen su ba bu babbaka wajen murdiya da danne masu hakki.
A yayin ci gaba da babatu shugaban kungiyar yakin neman zaben ya ce dan takara na jam'iyyar APC, Alhaji Ahmed Aliyu, shi ne ya cancanci hukumar INEC ta kaddamar tare da shellantawa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Sakkwato.
Cikin buga misali na abin da kowane mai hangen nesa zai fahimta, Alhaji Suleiman ya ce duba da yadda jam'iyyar APC ta yi nasara a jihar Sakkwato yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, akwai Lauje cikin nadi dangane da yadda sakamakon ya kaya a yayin zaben gwamna.
KARANTA KUMA: Za mu dauki shekaru fiye da 10 gabanin gyara barnar da Boko Haram ta haifar a Najeriya - Buhari
Alhaji Suleiman ya sha alwashin cewa jam'iyyar su ta APC za ta nemi hakkin ta agaban kotun daukaka kara inda ta ke kyautata zato gami sa ran za a tabbatar da adalci a sanadiyar gudunmuwar murdiya da hukumar INEC ta bayar domin rinjyar da nasara ga jam'iyyar PDP.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng