Na taba karbo $10m don na tabbatar ina da kudin da ake fada - Aliko Dangote

Na taba karbo $10m don na tabbatar ina da kudin da ake fada - Aliko Dangote

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewar ya taba fitar da zunzurutun kudi da adadinsu ya kai dalar Amuraka miliyan goma ($10m) domin kawai ya tabbatar wa da kansa cewar yana da arzikin da ake fada.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata hira da Mo Ibrahim, wacce aka yi a wurin taro na musamman a cibiyar Mo Ibrahim dake Abidjan, kasar Kwadebuwa.

A faifan bidiyon hirar da aka wallafa a shafin YouTube, Dangote ya bayyana cewar; "burin duk wanda ya fara kasuwanci shine ya mallaki miliyan ta farko. To, nima nayi hakan.

Na taba karbo $10m don na tabbatar ina da kudin da ake fada - Aliko Dangote
Aliko Dangote
Asali: UGC

"Bayan shekara guda, na fahimci cewar na tara kudi amma fa duk kudin a rubuce nake ganinsu, ba a zahiri ba.

DUBA WANNAN: Yadda za a raba arewa da talauci - Aliko Dangote

"Watarana sai kawai na je banki, a lokacin babu wasu dokoki da ka'idoji kamar yanzu, sai na cike takarda na fitar da $10m na saka ta a bayan mota na tafi da su gida domin kawai na kalle su. Sai a lokacin na tabbatar da cewar ina da kudi."

Dangote ya kara da cewa ya mayar da kudin banki washegari bayan ya kalle su ya more.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel