Buhari ya gana da Sarki Abdullahi Husseini II na kasar Jordan (Hotuna)

Buhari ya gana da Sarki Abdullahi Husseini II na kasar Jordan (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Sarkin Jordan, Sarki Abdullahi bin Al-Hussein II a bayan fagen taron tattalin arziki na yankin Gabas Ta Tsakiya da Afirka Ta Yamma da aka gabatar a birnin Amman na kasar Jordan.

Buhari ya mika godiyarsa ga Sarki Abdullahi bisa irin gudunmawar da ya ke bawa Najeriya wurin yaki da ta'addanci da ta ke yi.

Mai taimakawa shugaban kasa a fanin watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Abuja inda ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yabawa Sarki Abdullah II.

DUBA WANNAN: An kori diyar 'dan majalisar tarayya da aka gano tana aiki da takardun bogi

Hotunan ganawar Buhari da Sarki Abdullahi Hussein na Jordan
Shugaba Muhammadu Buhari da tawagarsa tare da Sarki Abdullahi Hussain II na kasar Jordan
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya ce goyon bayan da kasashen duniya ke bawa Najeriya, musamman kasar Jordan ya nuna cewa kasashen na duniya sun shirya hada kansu wuri daya domin zaman tsintsiya madaurinki daya wanda hakan zai haifar da zaman lafiya mai dorewa.

Hotunan ganawar Buhari da Sarki Abdullahi Hussein na Jordan
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Sarki Abdullahi Hussein na kasar Jordan
Asali: Twitter

Muhammadu Buhari zai bar Birnin Amman da ke kasar Jordan ne gobe Lahadi 7 ga Watan Afrilun 2019. Daga nan ne ake sa ran shugaban kasar na Najeriya zai gana da manyan kasar UAE a wani zama na musamman da za ayi.

Hotunan ganawar Buhari da Sarki Abdullahi Hussein na Jordan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganarwarsa da Sarkin kasar Jordan, Abdullahi Hussaini II
Asali: Twitter

Kamar yadda labari ya zo mana dazu nan, Mai Martaba Sarkin Dubai kuma Firayim Minista na kasar UAE, Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum, shi ne ya gayyaci shugaba Buhari zuwa taron da aka shirya a cikin kasar sa.

Za a yi wannan zama ne da manyan shugabannin Duniya game da harkar bunkasa tattalin arzikin kasashe ta hanyar shigowar hannun jari. Wannan zama da za ayi yana cikin manyan taron da aka saba gani na kasashen Duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel