Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili

Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili

A yanzu ne tauraruwar kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano CP Muhammad Wakili (Singham) ke kara haskawa tun lokacin da ya fara aiki a jihar ta Kano. Sai dai kuma mutane kalilan ne su ke da masaniya akan rayuwarsa

A wata hira da ya yi da manema labarai, ya bayyanawa manema labaran wasu sirrikan rayuwarsa, wadanda da yawa daga cikin masoyansa ba su sani ba.

Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili

Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili
Source: UGC

Wane abu ne ya fi ba ka tsoro?

"Abinda ya ke tayar mini da hankali shine yadda aikata manyan-manyan laifuka ya zama tamkar ruwan dare a wannan lokacin, yadda darajar ran dan adam ta zama tamkar ta sauro."

A wace jiha ce ka fi jin dadin aiki?

"Kar ki hada ni fada da mutane, ban zabi na zabe ba, amma Hajiya a Kano aka saka mini suna Singham, saboda haka ina jin dadin aiki matuka a Kano."

Menene ma'anar Singham?

"Na tambaya aka ce mini wani wasan kyakwayone na Indiya da al'ummarsu ta gurbace sai aka kawo wani dan sanda wanda ya ke aiki tukuru don ya gyara al'ummar, sai suka ga kamar aikin da na ke yi ya so yayi kama da nashi shi ne suka mini suna Singham."

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

Amma kana fatan kaga Singham din Indiyan?

"Aa ai sai dai shi ya neme dai."

Wane irin abinci ka fi so?

"Na fi son tuwo miyan kuka, duk wani abinci da na samu in dai ina jin yunwa larurace, amma idan kana so ka burgeni to ka bani tuwo miyan kuka."

Wane irin wasa ka fi so?

"Gaskiyar magana na fi son wasan kokawa."

Wace irin mota ka fi so?

"Wacce za ta daukeni ta kaini inda zanje ita na fi so, ba ruwa da kala ko kamfani, ni duk motar da za ta biya mini bukata ta a lokacin da na ke da ita na ke so."

Kana karbar cin hanci kamar yadda ake zargin 'yan sandan Najeriya su na yi?

"Cin hanci haramun ne, addinin ya fada mana abu kaza halal ne abu kaza haram ne. To duk sisi da Allah ya ce karbar ta haramun ce bana sha'awarta, kuma bana kaunar wani mutum ya karba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel