Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Wata matar aure mai suna Bilkisu Abubakar ta yanke jiki ta fadi ta mutu a yayin da take rikici da kishiyarta, Hajara Abubakar.

Matan biyu suna zaune ne a kauyen Jiramo da ke karamar hukumar Takai na jihar Kano.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba misalin karfe 10 na dare.

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta kare kanta a kan kisan 'yar Najeriya

Matar aure ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take fada da kishiyarta
Matar aure ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take fada da kishiyarta
Source: UGC

Ya ce dagajin kauyen ne ya tiso keyar wanda ake zargin, Hajara zuwa caji ofis.

A cewar wanda ake zargi, "ta samu rashin jituwa da kishiyarta ne wanda hakan ya janyo fada tsakaninsu, suna cikin fadan sai Bilkisu ta yanke jiki ta fadi ta mutu."

Ya ce an kai gawar matar da ta rasu zuwa dakin ajiye gawa na asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel