Jami’an kwastam sun jikkata Sojojin sama guda 2 a yayin rikici daya kaure a tsakaninsu

Jami’an kwastam sun jikkata Sojojin sama guda 2 a yayin rikici daya kaure a tsakaninsu

Wasu dakarun rundunar mayakan Sojan sama na Najeriya sun ga ta kansu a hannun jami’an hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam, bayan jami’an na kwastam sun lakada jikkatasu sakamakon rikici daya kaure a tsakaninsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu a daidai shingen ababen hawa dake kan titin Badagry na jahar Legas, yayin da Sojojin suke tafiya a cikin wata mota kirar Toyota Camry suka isa shingen.

KU KARANTA: Kalli yadda Buhari ya shiga kasar Jordan

Isarsu keda wuya sai suka shaida ma jami’an hukumar kwastam cewa su fa Sojoji ne, kuma babu wani abin haramci a cikin motarsu, amma jami’an suka dage kai da fata cewa lallai sai sun binciki motar ciki da bai.

Daga nan aka fara cacan baki har ta kai ga an baiwa hammata iska a sanadiyyar Sojojin sun yi kokarin kwace bindigun dake hannun jami’an na kwastam, sai dai basu samu nasara ba, inda jami’an suka lakada musu dan banzan duka, suka raunata Soja daya a kai, dayan kuma a hannu.

An bayyana sunayen Sojojin da suka ci dukan kamar haka; kofur Waziri da kofur Chidi Onyecheke, amma fa su ma jami’an na kwastam basu tsaya wata wata ba, inda suka tattara inasu inasu suka tsallake daga shingen don gudun fushin Sojoji.

Daga bisani an garzaya da Sojojin zuwa asibtin Mother and Child dake dake cikin sansanin Sojojin sama dake Ahanve cikin unguwar Badagry don basu kulawar data dace. Shima kaakakin kwastam na reshen Seme, Saidu Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace ba a karkashinsu jami’an suke ba.

Sai dai ya bada tabbacin hukumar zata nemi zama da hukumar sojan sama don tattauna batun tare da lalubo hanyar sulhu da maslaha don amfanin kowa da kowa, tare da kare aukuwar lamarin a gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel