Jam'iyyar APC za ta dawo da kimar da ta ke da ita a jihar Sokoto - Wamakko
A dai-dai lokacin da jam'iyyar PDP ta ke murnar lashe zabe a jihar Sokoto, sai gashi Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko yana yi wa 'yan jam'iyyar APC albishir da cewa jam'iyyar APC zata karbe mulki daga hannun PDP a jihar Sokoto
'Yan jam'iyyar APC na jihar Sokoto sun cika da farin cika, bayan da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya tabbatar musu da cewar za su karbi kujerar gwamnan jihar daga hannun jam'iyyar PDP.
Wamakko, wanda ya yi bayanin a gidansa da ke Gowon Nama cikin jihar Sokoto, bayan dawowar shi daga Abuja jiya Laraba, ya ce yana da tabbacin cewa za su samu nasarar karbar kujerar gwamnan.
A lokacin da yake yi wa taron 'yan jam'iyyar bayani, Wamakko ya ce, duk da sun da cewar Allah ne ya ke bada mulki kuma ya karbe daga hannun duk wanda ya ke so, sai dai yana da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba mulki zai dawo hannunsu.
Sanatan ya ce, "Ina da tabbacin cewa, za mu dawo da mutuncin jam'iyyar mu. Allah yana bada mulki kuma ya karbe abin shi, saboda haka Allah ya riga ya bamu.
"Ina rokon 'yan jam'iyya da su kwantar da hankulansu, sannan su zamanto ma su bin doka da oda, su daina ta da rikici a cikin al'umma.
KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano
"Allah ne kadai ya ke bayar da mulki, kuma ina da tabbacin cewa kokarin da jam'iyyar mu ta yi ba zai tashi a banza ba. Zamu ci ribar abinda muka yi nan ba da dadewa ba."
A karshe Sanatan ya yabawa 'yan jam'iyyar da irin kokarin da suka dinga yi na azumi da salloli, saboda jam'iyyar ta samu nasara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng