Wani masanin fina finan Hausa ya yi karin haske kan ikirarin Adam Zango

Wani masanin fina finan Hausa ya yi karin haske kan ikirarin Adam Zango

Fitaccen marubuci, tsohon dan jarida, kuma masanin harkar fina finan Kannywood a Najeriya, Malam Ibrahim Sheme ya fede ikirarin da jarumin jarumai na fina finan Kannywood, Adamu A Zango yayi na cewa shine bahaushen da yafi shahara a duniya.

Sheme ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC Hausa, inda yace wannan wata dabarace na neman ma kai suna, ta yadda jama’a zasu cigaba da tafka muhawara akansa, tare da tunashi, hakan zai sa ba zasu manta da shi ba.

KU KARANTA: Zargin kisan mijinta: Maryam Sanda za ta san matsayinta a yau

Wani masanin fina finan Hausa ya yi karin haske kan ikirarin Adam Zango
Sheme da Adam Zango
Asali: UGC

Legit.ng ta ruwaito Sheme yana danganta da abinda Zango yayi ga wani batu da marigayi dakta Mamman Shata ya taba yi, inda yace wasu wakokinsa zasu bace idan ya mutu, wanda hakan yasa aka yi ta tafka muhawara akan wannan magana.

Haka zalika Sheme ya kara da cewa a yanzu dai tauraruwar Adam Zango ta fara yin kasa, kamar yadda ita kanta harkar Fim din take kasa, don haka yake neman hanyoyin da zasu kara ma kansa likafa, kamar yadda ya taba yi lokacin daya daura Al-Qur’ani akai yayi rantsuwa a gidan talabijin.

Bugu da kari Sheme ya musanta wannan ikirari na Zango, inda yace kamata yayi a auna shi da Hausawa, kuma Hausawa suna da yawa, akwai wadanda suka mutu da wadanda suke raye, kuma akwai wadanda suka shahara a fage daban daban na rayuwa, don haka har sai kayi wannan gwaje gwajen zaka gane.

Marubucin ya kawo wasu mutane kamarsu shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan kwallon kafa Ahmed Musa, wanda yace sun fi Zango shahara a Duniya, hakanan yace zayyano sunayen Ali Nuhu, Rahama Sadau, Hadiza Gabon a matsayin wadanda suka fi Zango yawan mabiya ko a shafin Instagram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel