Fayose ya taya ‘Amini’ Wike murnar sake lashe zaben Gwamna a PDP

Fayose ya taya ‘Amini’ Wike murnar sake lashe zaben Gwamna a PDP

Ayodele Fayose wanda shi ne wanda ya bar gadon mulkin jihar Ekiti ba da dadewa ba, yayi magana bayan da aka kammala zaben gwamna a jihar Ribas inda jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasara.

Mista Ayo Fayose, yayi jawabi a shafin sa na sada zumunta na Tuwita, inda ya taya gwamna mai-ci Ezenwo Nyesom Wike da mutanen jihar Ribas nasarar da jam’iyyar PDP ta sake samu a zaben gwamna na wannan karo.

Fayose yake cewa nasarar da Gwamna Wike ya samu, ya nuna cewa mutanen Najeriya za su iya tsayawa tsayin-daka, su jajirce wajen ganin zabin su yayi amfani duk da irin kama-karyar da damukaradiyya ta ke fuskanta a kasar.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Gwamnan Jihar Ribas Mai nasara Wike

Fayose ya taya ‘Amini’ Wike murnar sake lashe zaben Gwamna a PDP
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Fayose ya ji dadin zaben Ribas
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan yake cewa wannan nasara da PDP ta samu yayi masa dadi, ganin yadda wasu marasa kishin Ribas su kayi kokarin maida jihar, wajen zubda jini da sunan zabe. Fayose bai dai kama sunan wanda yake nufi ba.

Yadda mutanen jihar Ribas su ka rike gwamna Wike da PDP duk da irin barazanar mutuwa da su ka fuskanta a zaben da aka yi, ya nuna cewa ‘Yan Najeriya su na iya jajircewa domin damukaradiyya ta habaka inji Fayose.

A ranar 3 ga Watan Afriku, INEC ta tabbatar da cewa PDP ta lashe zaben gwamna a jihar Ribas, hakan yayi Mista Ayodele Fayose wanda yana cikin manyan ‘yan adawar gwamnatin jam’iyyar APC dadi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng