Wasu daliban sakandare sun kirkiro wata fasaha da za ta rage cunkoson motoci a Najeriya

Wasu daliban sakandare sun kirkiro wata fasaha da za ta rage cunkoson motoci a Najeriya

- Wasu dalibana makarantar sakandare sun kirkiro wata fasaha da zata rage cunkoson ababen hawa a Najeriya

- Wata kungiya da ta ke taimakon daliban sakandare ita ce ta taimakawa daliban wurin cika burin na su

Daliban makarantar Sakandaren Caro Favoured Schools, da ke unguwar Ajegunle cikin jihar Lagas, sun kirkiri wata sabuwar fasaha wacce za ta rage cunkoson ababen hawa a hanyoyin kasar nan.

Daliban wadanda su ke ajin karshe a makarantar, sun bayyana sunayensu kamar haka; Blessing Omosebi, Sarah Onabanjo, Uchechukwu Fedricks da kuma Emmanuel Anyanwu.

Daliban sun kirkiri irin fitalar nan ta kan titi wacce zata dinga amfani da hasken rana a duk lokacin da babu haske a guri.

Daliban sun bayyana cewa fasahar kirkirar ta su ta zo musu ne ta dalilin cunkoson da suke gani a duk lokacin da za su je makaranta da kuma bayan sun tashi daga makaranta.

Wasu daliban sakandare sun kirkiro wata fasaha da za ta rage cunkoson motoci a Najeriya
Wasu daliban sakandare sun kirkiro wata fasaha da za ta rage cunkoson motoci a Najeriya
Asali: UGC

A cewarsu bayan sun bayyana fasahar ga junansu, ba su san daga ina za su fara ba, don ganin sun cimma burinsu, har sai da suka samu labarin kungiyar da ta ke taimakawa yara masu fasaha mai suna Junior Achievers of Nigeria a turance. Kungiya ce da ta ke taimakawa dalibai masu fasaha wurin ganin sun cika burinsu na kirkire-kirkire.

Daliban su ka ce: "Bayan sun shiga kungiyar (JAN), kungiyar ta taimaka musu matuka wurin ba su taimako na kudi, sannan kungiyar ta kara wayar musu da kai akan irin yadda za su dinga kawo fasaha ta sababin kirkire-kirkire, domin samun cigaba a rayuwa."

KU KARANTA: 'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, Emmanuel Anyanwu ya ce: "Matsalolin yankin Afirka suna da yawa amma matsalar hanyoyi da ababen hawa suna daya daga cikin manyan matsalolin da kasar nan take fuskanta. Saboda haka ne suka kirkiro fasahar da za ta kawo saukin cunkoso, sannan kuma ta kawo cigaba a kasar nan.

"Fasahar mu tana amfani da hasken rana, bata bukatar wutar lantarki, in dai akwai hasken rana fitilar ta mu za ta yi caji sosai wanda za a iya amfani da ita na kwanaki da yawa ba tare da an sake neman ayi mata caji ba.

"Bayan mun kirkiri fitilar ta mu munyi gasa da wasu daga cikin 'yan kungiyar (JAN), inda mu ka lashe gasar. Kungiyar ta (JAN) wacce ta fara aiki a kasar Amurka shekaru 100 da suka gabata, inda a yanzu haka shekarar ta 20 da fara aiki a Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng