Kadan daga cikin tarihin Gwamnan Ribas da zai zarce a mulki

Kadan daga cikin tarihin Gwamnan Ribas da zai zarce a mulki

A jiya ne hukumar zabe na INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Nyesom Wike na jam’iyyar PDP a jihar Ribas. Nyesom Wike yayi wa babban Abokin hamayyar sa na jam’iyyar AAC mugun duka a zaben gwamnan jihar da aka yi.

Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin wannan fitaccen Gwamna:

1. Haihuwa

An haifi Ezenwo Nyesom Wike CON ne a cikin Disamban 1967. Nyesom Wike asalin sa mutum Kabilar Ikwere ne da ya fito daga yankin Rumuepirikom da ke cikin karamar hukumar Obio-Akpor.

2. Siyasa

Nyesom Wike ya shiga siyasa ne tun yana Matashi shakaf, a 2007 ne ya samu shiga cikin manyan gwamnatin jihar Ribas bayan da Rotimi Amaechi ya nada sa a matsayin Sakataren gwamnati.

3. Minista

Daga baya Rotimi Amaechi ya aika sunan Nyesom Wike a matsayin Minista a gwamnatin Jonathan inda ya rike karamin Ministan ilmi. Daga baya kuma aka nada Wike Mukaddashin babban Ministan ilmi.

KU KARANTA: APC tayi kuskuren hana ni takarar Gwamnan Imo a 2019 – Nwosu

Kadan daga cikin tarihin Gwamnan Ribas da zai zarce a mulki
Nyesom Wike na Jihar Ribas ya sake lashe zaben Gwamna
Asali: Depositphotos

Kafin wa’adin sa ya cika ne yayi murabus ya nemi takarar gwamna a jihar Ribas a zaben 2015 karkashin PDP. Wannan ya sa shugaba Goodluck Jonathan ya maye gurbin sa da wani Ministan a 2014.

4. Rikici da Mai Gidan sa

Wike ya samu sabani da Gwamna a lokacin sa Rotimi Amaechi bayan an nada sa Minista a 2011. Daga karshe Wike yayi zaman sa a PDP bayan Amaechi da jama’an sa sun koma jam’iyyar APC.

5. Gwamna

Mista Nyesom Wike yayi takarar gwamna ne a 2015 inda ya tika Dr Dakuku Peterside na APC da kuma Tonye Princewill na LP da kasa. An yi ta fama a kotu wanda a karshe PDP ta samu nasara.

A Watan Afrilu ne INEC ta tabbatar da cewa Nyesom Wike zai zarce a kan mulki bayan ya lashe zaben jihar da aka yi. A wannan zabe Kotu ta hana APC shiga a dama da ita bayan an rushe zaben ta.

6. Iyali

Mai dakin gwamna Nyesom Wike ita ce Eberechi Wike wanda Alkali ce a babban kotun tarayya da ke jihar Ribas. Shi ma dai gwamnan ya karanta ilmin shari’a ne a Jami’ar fasaha ta jihar Ribas. Wike su na da 'Ya 'ya 3 a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel