Yadda za a raba arewa da talauci - Aliko Dangote

Yadda za a raba arewa da talauci - Aliko Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote sannan attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya ce yankin arewacin Najeriya zai cigaba da zama cikin talauci matukar gwamnatocin jihohin yankin basu cike gurbin tazarar cigaba dake tsakanin yankin da takwaransa na kudu ba.

Da yake magana yayin bikin kaddamar taron bunkasa kasuwanci a jihar Kaduna, karo na hudu (KadInvest 4.0), Dangote ya caccaki gwamnonin arewacin Najeriya a kan rashin bawa yaki da talauci fifiko.

A cewar sa: "Najeriya ce kasa ta 157 a cikin jerin kasashe 189 dake fama da karancin cigaba. Duk da akwai talaucin da ke Najeriya abin damuwa ne, akwai banbanci mai girma ta fuskar mizanin talauci a tsakanin bangarorin kasar.

"A yankin arewa maso yamma da arewa maso kudu, fiye da kaso 60% na mutanen yankin suna zaune cikin kungurmin talauci.

"Abin takaici ne a ce yankin arewacin Najeriya mai jihohi 19 da fiye da kaso 54% na yawan mutanen Najeria, amma ya samar da kaso 21% ne kawai na kudaden shiga da gwamnati ta samu a shekarar 2017.

Yadda za a raba arewa da talauci - Aliko Dangote

Aliko Dangote
Source: UGC

"Yankin arewa zai cigaba da zama a cikin halin talauci matukar gwamnatocin jihohi basu yi hobbasa wajen cike gurbin da ya banbanta kudu da arewa ba ta fuskar cigaba.

"Hakan ne yasa koda yaushe muke magana a kan babban kalubalen da ke damun mu, kuma ina fatan arewa zata samu gwamnoni 10 irin Malam Nasir El-Rufa'i domin su kawo cigaba arewa.

DUBA WANNAN: Abinda yasa mambobin jam'iyyar suka ki zuwa karbar shaidar cin zabe a Kano - PDP

"Cike gurbin tazarar dake tsakanin arewa da kudu yana bukatar saka jari a bangaren kasuwanci na shekaru masu yawa, bangaren da ba na gwamnati bane kawai zai iya samar da kudaden da kasar nan ke bukata domin bunkasa kasuwanci.

"Akwai bukatar gwamnati ta saukaka tare da bullo da tsare-tsaren da zasu jawo hankalin masu saka jari a bangaren kasuwanci da kafa masana'antu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel