PDP ta lashe zaben gwamnan jihar Ribas, INEC ta sanar

PDP ta lashe zaben gwamnan jihar Ribas, INEC ta sanar

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da sunan Nyeson Wike a matsayin dan takarar da ya lashe zaben gwamnan jihar Ribas da aka ammala tattara wa a yau, Laraba.

Wike, gwamna mai ci kuma dan takarar jam'iyyar PDP, ya samu jimillar kuri'u 886,264 da suka bashi nasarar zama zakara a zaben gwamnan jihar Ribas.

Biokpomabo Awara, dan takarar jam'iyyar AAC da Rotimi Amaechi ke goya wa baya ya samu jimillar kuri'u 173,859 kacal.

Jimillar sakamakon ta nuna cewar gwamna Wike ya samu nasara a kan babban abokin hamayyarsa da tazarar kuri'u 712,405.

A lokacin da INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar a jiya, Talata, bayan karbar sakamako daga kananan hukumomi 15, Wike ne a kan gaba da adadin kuri'u 426,369 yayin da Awara ke biye masa da adadin kuri'u 129,855.

Jam'iyyar APC ba ta da dan takarar gwamna a jihar Ribas. Hakan ya biyo bayan gaza gudanar da zaben fidda 'yan takara da jam'iyyar tayi a kan lokaci.

Hakan ne yasa jagoran jam'iyyar APC a yankin kudu maso kudu kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewar magoya bayan APC su zabi jam'iyyar AAC a zaben gwamnan jihar.

INEC ta dakatar da dukkan wasu harkokin da suka shafi zaben gwamna a jihar Ribas bayan an samu barkewar rikici a sassan jihar da dama yayin gudanar da zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki na ranar 16 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel