An harbe masu garkuwa da mutane guda 3 a Kaduna

An harbe masu garkuwa da mutane guda 3 a Kaduna

A wata arangama da aka yi tsakanin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, rundunar 'yan sandan ta samu nasarar harbe mutane uku a cikin 'yan ta'addar

A yau Larabar nan ne 3 ga watan Afrilu rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ba da sanarwar cewar ta harbe wasu mutane uku da ake zargin 'yan garkuwa da mutane ne, wadanda suka yi kokarin shiga cikin kamfanin gine-gine na Mother Cat da ke unguwar Mando, cikin garin Kaduna.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Mista Onah Sunny, shi ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Kaduna.

Sunny ya ce lamarin ya faru ranar Larabar nan da misalin karfe 5:40 na asuba, a lokacin da jami'an 'yan sanda suka gano 'yan ta'addaar suna kokarin shiga kamfanin.

An harbe masu garkuwa da mutane guda 3 a Kaduna
An harbe masu garkuwa da mutane guda 3 a Kaduna
Asali: UGC

"Jami'an mu sunyi artabu da 'yan ta'addar inda su ka samu nasarar harbe mutane uku daga cikin su.

"A lokacin da su ke musayar wutar da 'yan ta'addar, jami'in mu Insp. Bijimi Maiyaki da Kabiru Shu'aibu sun ji raunika, in da a yanzu haka suna asibitin 44 suna karbar magani.

"Bayan haka kuma, daya daga cikin 'yan sandan da suke karbar maganin ya rasa ransa," in ji Sunny.

KU KARANTA: 'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa jami'an sun samu damar kwato makamai daga wurin 'yan ta'addar. Sannan ya kara da cewa a yanzu haka jami'an 'yan sandan suna nan suna neman inda sauran 'yan ta'addar suke.

"Ina rokon al'umma da su taimakawa jami'anmu da duk wani bayani na mutanen da ba a san su ba a kowane yanki suke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel