Kotu tayi watsi da karar da aka shigar a kan zababen gwamnan jihar Borno

Kotu tayi watsi da karar da aka shigar a kan zababen gwamnan jihar Borno

Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Maiduguri tayi watsi da karar da aka shigar na neman soke zaben fidda gwani da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi a jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Mamman Durkwa ne ya shigar da karar a ranar 19 ga watan Disamban 2018 inda ya ke kallubalantar nasarar da Babagana Zulum ya yi na zaben cikin gidan na APC da aka yi a ranar 30 ga watan Satumban 2018.

Mr Zulum wanda Farfesa ne ya yi nasarar lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihar ta Borno.

DUBA WANNAN: Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa su yi

Kotu tayi watsi da karar da aka shigar a kan zababen gwamnan jihar Borno
Kotu tayi watsi da karar da aka shigar a kan zababen gwamnan jihar Borno
Asali: Twitter

Durkwa ya shigar da jam'iyyar APC da INEC ne kara a kotu na neman a soke zaben da ta bawa Zulum damar zama dan takarar jam'iyyar APC.

A yayin da ya ke yanke hukunci, Alkalin kotun, Jude Dagat ya yi watsi da karar ne saboda ba a shigar da ita a cikin wa'adin kwanaki 14 ba kamar yadda Dokar Zabe ta tanada.

Mr Dagar ya ce an shigar da karar ne bayan wa'addin da doka ta diba ya kare.

Wannan ya sa alkalin ya yi fatali da karar kuma ya bayar da wa'addin kwanaki 30 domin bawa wanda ya shigar da karar daukaka kara.

Lauya mai kare wanda akayi kara, Abdulwasiu Alfa, ya bayyana murna a kan hukuncin da kotu ta yanke yayin shi kuma lauyan mai kara, Usman Abubakar ya ce za su daukaka karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel