An yi garkuwa da Matafiya 37 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

An yi garkuwa da Matafiya 37 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a Yammacin ranar Litinin da ta gabata, ana zargin wasu Matafiya kimanin 37 sun afka cikin tarkon masu ta'adar garkuwa da mutane a kan hanyar birnin Abuja zuwa Kaduna.

Sahihan tushen rahoto na hukumomin tsaro sun shaidawa manema labarai cewa, mummunan lamarin ya auku da misalin karfe 9.00 na yammacin Litinin a kauyen Garin Gosa da ke mararrabar hanyar Kaduna da Abuja.

An yi garkuwa da Matafiya 37 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna
An yi garkuwa da Matafiya 37 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Kanduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar wannan mugun ji da mugun gani na ta'adar garkuwa, sai dai ya gaza bayar da tabbaci kan adadin mutane da lamarin ya ritsa da su.

Babban jami'in na 'yan sanda ya bayar da shaidar da cewa, binciken su ya kai ga tsinto wata Mota kirar Toyota Hilux kunshe da takarda shaidar karbar kudi a banki da kuma takalman Mata a kauyen Gidan Busa da ke da tazara ta kilomita kimanin arba'in da birnin Kaduna.

KARANTA KUMA: Farashin Man Fetur ya yi daraja a kasuwar duniya

A yayin majiyoyin rahoton da dama suka raja'a akan adadin mutane 37 da aka yi garkuwa da su, rahotanni sun bayyana cewa kawowa yanzu ba bu wanda masu ta'adar suka tuntuba domin neman kudin fansa ko makamancin haka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel