An kama wasu 'yan Najeriya 5 da suka yi fashi da makami a kasar Dubai
- 'Yan sandan birnin Sharjah na kasar Dubai sun sanar da kama wasu 'yan Najeriya biyar da laifin fashi da makami
- Waadanda ake zargin sun balla shagon masu canjin kudaden kasashen ketare inda suka yi awon gaba da makudan miliyoyi
- An kama masu laifin cikin kasa da sa'a 48 bayan jami'an 'yan sanda sun shiga farautar su
An kama wasu 'yan Najeriya biyar da ake zargi da aikata laifin fashi da makami a kasuwar canjin kudi da ke Sharjah a hadaddiyar daular larabawa (UAE) da aka fi kira da Dubai.
Rahotanni sun bayyana cewar wadanda ake zargin sun yi awon gaba da kudaden kasashen ketare da yawansu ya kai Dhirhami miliyan Dh2.3, fiye da Naira miliyan N226 a kudin Najeriya.
A cewar 'yan sanda a garin Sharjah, mutanen sun balle kofar shagon masu canjin kudade tare kwasar kudaden kasashe daban-daban da suka tsere da su.
DUBA WANNAN: Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara
Wadanda ake zargin sun raunata wasu ma'aikatan kasuwar canjin da suka yi kokarin dakile yunkurinsu. Daya daga cikin ma'aikatan ne ya sanar da jami'an 'yan sanda.
Jami'an 'yan sandan sun yi nasarar kama masu laifin a cikin kasa da kwana biyu bayan sun hada kai da abokan aikinsu da ke Abu Dhabi, Ras Al Khaimah da Anjam.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng