Bayyanar juna biyu bayan mutuwar aure: Wata matashiya, Bilkisu ta shigar da karar tsohon mijin ta

Bayyanar juna biyu bayan mutuwar aure: Wata matashiya, Bilkisu ta shigar da karar tsohon mijin ta

Bilkisu Aminu, wata matashiya mai shekaru 28, ta shigar da karar tsohon mijinta, Muhammad Jibril, a gaban wata kotun shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna a kan kin amincewa da juna biyu da take dauke da shi.

Bilkisu, mazauniyar cikin garin Kaduna, ta shaida wa kotun cewar ta zauna tare da Jibril na tsawon wata uku kafin daga bisani aurensu ya mutu.

"Ya sake ni a ranar 6 ga watan Fabrairu, amma bayan nayi kwana biyu a gida sai na yanke shawarar zuwa asibiti domin a yi min gwaji, bayan an yi gwajin ne likita ya tabbatar min cewar ina dauke da juna biyu.

"Amma bayan na kira Jibril na sanar da shi maganar juna biyun, sai ya ce zai ziyarce ni amma har yanzu shiru," a cewar Bilkisu.

Bayyanar juna biyu bayan mutuwar aure: Wata matashiya, Bilkisu ta shigar da karar tsohon mijin ta
Bayyanar juna biyu bayan mutuwar aure: Wata matashiya, Bilkisu ta shigar da karar tsohon mijin ta
Asali: UGC

Jibril, mai shekara 32, mazaunin titin Zaria a garin Kaduna, ya shaida wa kotun cewar juna biyun ba nasa ba ne.

Ya ce bai sadu da Bilkisu ba a tsawon watanni biyu da su ka zauna tare.

DUBA WANNAN: Ana wata ga wata: Wata matar aure mai suna Hajara ta mutu a dakin saurayin ta

"Bamu taba kwanciyar aure tare ba a 'yan watannin da muka yi tare. Saboda yawan matsalolin da ke tsakanin mu, a cikin wata na uku da auren mu ne na sake ta," a cewar Jibril.

Alkalin kotun, Musa Sa'ad-Gona, ya bayar da umarnin a raka tsofin masoyan asibiti domin gudanar da gwajin juna biyu a kan Bilkisu kafin ya fara sauraron karar ranar Alhamis mai zuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel