Wata sabuwa inji yan caca: An baiwa dalibai lasisin shan sigari don fahimtar darasi

Wata sabuwa inji yan caca: An baiwa dalibai lasisin shan sigari don fahimtar darasi

Bambarakwai, wai namiji da suna Hajara, inji masu iya magana, haka zalika dama Hausawa sun ce inda ranka ka sha kallo, kamar yadda jama’a ke ta mamakin wani matakin fahimtar darasi da wata jami’a ta samar ma dalibanta.

Wannan mataki shine na baiwa daliban jami’ar damar zukar taba ko sigari a cikin aji don su samu kyakkyawar fahimtar darussan da Malamansu ke koya musu, a jami’ar noma ta Yunan Agricultural Unversity dake kasar China.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya aurar da yayansa mace da namiji a Lafiya

Wata sabuwa inji yan caca: An baiwa dalibai lasisin shan sigari don fahimtar darasi
Daliban
Asali: UGC

Hotunan daliban jami’ar da dama sun wanzu a shafukan sadarwar zamani, yayin da suke banka ma sigari wuta suna zukarta a lokacin da suke tsaka da daukan darasi a cikin aji, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Sai dai ba wai haka nan bane hukumar jami’ar ta baiwa wadannan daliban lasisin shan sigari a cikin aji ba, illa tayi hakan ne a lokacin da ake koyar da daliban darasi akan ganyen tabar sigari, amfaninta da illolinta.

Shugaban sashin kula da harkokin dalibai na jami’ar, Zhao Zhengdiong ya tabbatar da cewar an dauko hotunan daliban ne a lokacin da suke daukan darasi akan ganyen taba, inda yace iyaka a lokacin darasin aka basu damar shan sigarin, daga nan kuma aka dakatar dasu.

Sai dai suma daliban jami’ar sun bada kariya ga kawunansu game da jita jitan da ake yadawa a shafukan sadarwa game dasu, inda suka ce sun zuki sigarin ne kawai don fahimtar darasin da ake musu akan shan taba sigari, inda suka ce darasin na da matukar muhimmanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel