Za ayi dashen kan mutum karo na farko a duniya

Za ayi dashen kan mutum karo na farko a duniya

- Wannan shine karo na farko kenan a duniya da za a fara gabatar dashen kan mutum

- Masanan sun fara gabatar da gwaji akan wani biri da kare, kuma gwajin na su ya yi yanda su ke so

Wasu masana a fannin kimiyya, Farfesa Sergio Canavero, da Xiaoping Ren, sun sanar da cewa sun gano hanyar da za a iya yiwa mutum dashen kai.

A lokacin da su ke bayani akan binciken na su, masanan sun tabbatar da cewa sun gama shiryawa tsaf don fara gabatar da dashen kan. Sannan masanan wadanda su ne na farko da za su fara yin aikin dashen kai a duniya, sun ce suna samun cigaba sosai a binciken da su ke yi.

Za ayi dashen kan mutum karo na farko a duniya
Za ayi dashen kan mutum karo na farko a duniya
Asali: Facebook

Masanan sun fara gabatar da binciken na su akan wasu dabbobi guda biyu, inda suka yi gwaji akan biri da kare, a karshe kuma dabbobin sun ta shi, suna harkokinsu.

Masanan sun gabatar da binciken na su a jami'ar Kimiyya da ke kasar China.

KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

A halin yanzu dai akwai mutum daya da ya yadda a fara gabatar da aikin a kanshi, mutumin wanda dalibi ne a fannin na'ura mai kwakwalwa, dan shekara 33, mai suna Valery Spiridonov, ya amince da masanan su gabatar da aikin akan shi saboda ciwon da yake da shi a jikinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng