Batsa: Mazauna Kaduna sun koka da masu tallar magungunan gargagiya

Batsa: Mazauna Kaduna sun koka da masu tallar magungunan gargagiya

Mazauna birnin Kaduna sun koka a kan irin kalaman batsa da batanci da mafi yawanci masu tallan magungunan gargajiya suke amfani da shi a yayin da suke tallata magungunansu.

Al'ummar garin Kaduna sun bayyana bacin ransu a kan lamarin a hirar da kamfanin dillancin labarai NAN, tayi da mutane daban-daban a ranar Asabar a jihar.

Daya daga cikin mazauna garin, Musa Goro da ke zaune a unguwar Tudun Wada ya ce abin takaici ne yadda masu tallar magungunan gargajiyar ke amfani da kallaman batsa yayin tallan magungunan.

DUBA WANNAN: INEC ta tsayar da ranar bawa Ganduje da 'yan majalisun jiha takardun shaidan cin zabe

Batsa: Mazauna Kaduna sun koka da masu tallar magungunan gargagiya
Batsa: Mazauna Kaduna sun koka da masu tallar magungunan gargagiya
Asali: Twitter

"Kalaman da wadannan masu tallan magungunan gargajiyan ke amfani da su wurin tallan kayayakinsu ba su da dadin ji, sun sabawa addini da kuma al'addun mu.

"Maganar gaskiya itace, kalmomin sun sabawa tarbiya, da addini da tsarin rayuwa ta mutanen kirki," inji shi.

Shi kuma Rabiu Muhammad da ke zaune a Kinkinau ya ce masu tallan magunguna sukan yi amfani da na'urar amsa kuwwa (loudspeaker) inda suka furta kalmomin marasa dadin ji ba tare da la'akari da cewa kananan yara suna sauraron su ba.

"Mutanen nan ba su da kunya, za ka ga suna amfani da loudspeaker suna fadin kalmomin da ba su dace ba a gaban kananan yara, mata da dattawa; wannan ya sabawa al'addun mu.

"Gaskiya ya kamata hukumomin da nauyin ya rataya a kansu su saka wata doka na gyara lamarin," a cewar Muhammad.

Wani malamin addinin musulunci, Zakariyya Usman ya ce galibi masu sayar da magungunan su kan zo tallar magani masallatan da ake sallar Juma'a.

"Abin takaici ne yadda masu sayar da magani ke talla a wuraren ibada; mu kan yi wa'azi a kan irin kalamansu da kuma hukuncin yin hakan a addini.

"Za a yiwa kowa hisabi a kan duk abinda ya furta da bakinsa a ranar kiyama, ya fi zama alheri mutum ya yi shiru a maimakon ya fadi magana mara dadi.

"Ya kamata a kafa doka da zata rika kulawa da yadda ake tallan magungunan gargajiya; Mu namu gargadi ne kuma munyi," inji Mallam Usman.

Wasu sauran al'umma da dama sun bayyana ra'ayoyinsu a kan lamarin inda suka ce irin kalaman da masu tallar ke furtawa yana gurbata tarbiyyar yara da matasa kuma su kayi kira ga hukuma ta dauki mataki a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel