An cafke wani malamin makaranta da ya ke lalata da dalibanshi
- Matsala ta lalata da dalibai dai ta zama ruwan dare a kasar nan musamman a makarantun gaba da sakandare
- Sai dai an bukaci gwamnati da ta dauki kwakkwaran mataki akan irin wannan lamarin, amma har ya zuwa yanzu babu wani canji da aka samu
Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta cafke wani malamin makarantar Sakandare da ta ke zargin shi da yi wa daliban makarantar da ya ke koyarwa dole wurin ganin sun ba shi hadin kai ya yi lalata da su.
Ana tuhumar malamin da aikata lalata da wata dalibarsa mai shekaru 18, inda ya yi mata alkawarin zai kara mata makin jarrabawa, idan ta ba shi hadin kai.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta jihar Legas, DSP Bala Elkanah shi ne ya tabbatar da cewar sun kama malamin, wanda su ke tuhumar shi da karawa dalibar mai shekaru 18 a duniya makin jarrabawarta, bayan ya gama tilasta ta akan ta yi lalata da shi.
Sai dai kuma majiyarmu LEGIT.NG ta samu labarin cewa kafin a kama malamin da wannan laifin, ya sha tilasta wadansu daliban na shi don su yi lalata da shi.
KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi
Ba wannan ne karo na farko ba da aka kama malami mai irin wannan hali, matsala ta lalata da dalibai ta zama ruwan dare a kasar nan, musamman a makarantun jami'a.
Wannan lamarin ne ma ya sa wata babbar kungiya da ta ke yaki da tilasta yin lalata da mata ta saka baki a cikin lamarin, inda ta bukaci ma'aikatar ilimi ta jihar Legas, tare da hukumar 'yan sandan jihar da su gabatar da kwakkwaran bincike akan lamarin.
Sannan kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar Legas da ta canjawa dalibar makaranta, domin gujewa kyama a cikin 'yan uwanta dalibai.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng