An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

- An iske gawar wata mata, tare da ta diyarta jim kadan bayan mijinta ya yi tafiya zuwa wani kauye

- Hukumar 'yan sanda ta ce za ta yi bakin kokarinta domin kamo wadanda su ka aikata ta'addancin

Hukumar 'yan sanda a jihar Kebbi su na binciken kisan wata mata da diyarta mai shekaru uku a duniya, a kauyen Dole Kaina da ke karamar hukumar Dandi, a jihar ta Kebbi.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan, DSP Nafiu Abubakar ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a Birnin Kebbi.

An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi
An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi
Asali: Twitter

A bayaninshi, ya bayyana cewa mijin matar mai suna Malam Zayyanu, ya iske gawar matarshi mai suna Balkisu, wacce ke da shekaru 27 da kuma diyarta mai shekaru 3 a duniya, a lokacin da ya dawo daga tafiyar da ya yi.

KU KARANTA: Duniya ina zaki damu: A Jigawa wani saurayi ya cire kan dan uwanshi akan saniya

Jami'in ya ce an iske gawar matar da ta diyarta bayan mijin na ta ya yi tafiya zuwa kauyen Tsamiya.

Ya bayyana lamarin a matsayin abu marar dadin ji, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta yi iya bakin kokarinta wurin kama wandada su ka aikata wannan ta'addancin, domin yanke mu su hukuncin da ya da ce da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel