Satar yara: "Yan sanda sun kama mutane uku a Zuba ta Abuja

Satar yara: "Yan sanda sun kama mutane uku a Zuba ta Abuja

Rubdunar 'yan sanda a birnin tarayya, Abuja, ta ce ta kubutar da wasu yara biyu da ake zargin wasu matasa uku da sace wa a yankin Zuba.

Matasan uku da akama su ne: Nasiru Mohammed mai shekaru 20, Sale Bello mai shekaru 19, da Hassan Audu mai shekaru 20.

Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Bala Chiroma, ne ya gabatar da matasan ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba.

Ya ce yaran da aka sace; Seke mai shekaru 9 da Rejoice Godwin mai shekaru 7, 'ya'yan mutum daya ne da aka sace ranar 8 ga watan Maris a kauyen Yimi da ke Zuba, sannan an kubutar da su ne a Lambata da ke jihar Neja.

Kwamishinan ya kara da cewa an samu wasu bindigun baushe biyu a wurin matasan yayin da 'yan sanda suka kama su.

Satar yara: "Yan sanda sun kama mutane uku a Zuba ta Abuja
Sifeton rundinar 'yan sanda ta kasa; Adamu Lafiya
Asali: Original

Kazalika, Ciroma ya ce rundunar 'yan sanda a Abuja tayi nasarar kama wasu 'yan fashi biyar da ake zargi da yin sata a wani gida da ke rukunin gidajen 'Sun City' a yankin Galadimawa ta Abuja.

Wadanda aka kama din su ne: Ayuba Isaac mai shekaru 22, Philemon Yohanna mai shekaru 28, Johnson Moses mai shekaru 28, Oduola Dayo mai shekaru 28, da Paul Philip mai shekaru 22.

DUBA WANNAN: Kisan Musulmai 50: An gano kungiyar da maharin New Zealand ke yiwa biyayya

Ya bayyana cewar jami'an 'yan sanda sun kama daya daga cikin 'yan fashin a shataletalen unguwar Galadimawa, yayin da aka kama ragowar abokansa a maboyar su a ranar 3 ga watan Maris.

Ciroma ya ce daga cikin abubuwan da aka samu a wurin 'yan fashin akwai bindigu biyu da alburusai, wani karfe na musamman, wayar hannu da kudi N91,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel